Jami’an ýansanda na neman jikan Sir Ahmadu Bello Sardauna ruwa a jallo

Jami’an ýansanda na neman jikan Sir Ahmadu Bello Sardauna ruwa a jallo

Wata kotun shari’ar musulunci dake jihar Sakkwato ta bada umarni ga hukumar yansandan jihar data kamo mata jikan Sardauna, kuma Magajin garin Sakkwato, Alhaji Hassan Danbaba, a ranar juma’a.

Jami’an ýansanda na neman jikan Sir Ahmadu Bello Sardauna ruwa a jallo

Magajin garin Sakkwato, jikan Sir Ahmadu Bello Sardauna

NAIJ.com ta samo rahoton daga kamfanin dillancin labarai, NAN, wanda ta ruwaito Alkali Umar Sifawa ne ya bada umarnin, biyo bayan wata kara da mataimakin shugaban jam’iyyar APC yankin Arewa maso yamma, Alhaji Inuwa Abdulkadir ya shigar gabansa.

Abdulkadir ya shigar da Danbaba kotu ne kan tuhumarsa daya keyi da ci masa zarafi, inda yace ciki wata kasida da Danbaba ya rubuta a watan Agustan bara, ya bayyana mahaifinsa a matsayin ''bawan wata tsohuwa mai suna Gwoggo, da ta saye shi sulalla 2’. Abdulkadir ya shaida ma kotu cewar Danbaba yayi zargin wai bai baiwa mahaifiyarsa kulawar data dace ba, har ta rasu.''

KU KARANTA: Rundunar mayaƙan sojan ƙasa zata fara gasar sarrafa makamai a dajin Sambisa

Sai dai wanda ake kara, Danbaba, ya mika kokensa ga kotun, inda yace a bai kamata ta aika masa da sammaci kwanaki 2 kacal kafin saurarin karar ba, Lauyan Danbaba, Yusuf Dankofa ne ya bayyana ma kotu hakan, inda yace ita kanta kotun ta yi ma dokar jin bahasin kowane bangare karan tsaye.

Lauya Dankofa ya shaida ma kotu cewa tayi ma dokar da tace: “Duk wanda ake tuhuma da aikata mummuna laifi, yana da daman samun isashshen lokaci don shirya kare kansa,” karar tsaye.

Haka zalika Magajin garin Sakkwato, Danbaba ya sake aika ma kotu da wata korafi inda ya bukaci data dakata da sauraron karar dake gabanta, har sai an yanke hukunci dangane da karar daya shigar gaban babban kotun jihar daya shigar.

Sai dai lauyan Inuwa Abdulkadir, John Shaka ya bukaci kotu data yi watsai da bukatun Danbaba, sa’annan ya bukaci kotu data umarci shugaban yansandan Najeriya daya kamo Danbaba a duk inda yake, kuma ya gurfanar da shi gaban kotu.

Dayake yanke hukunci, Alkali Sifawa yayi watsi da bukatar wanda ake kara, sa’annan yace: “Bai kamata ayi watsa da karar dake gabana ba, amma zamu kara ma wanda ake kara lokaci daya bayyana don ya kare kansa inda yaso.”

Sa’annan Alkali mai shari’a yace dangane da baiwa yansanda umarni: “Ina sanar da cewa za’a bada izinin neman mai laifi ga yansanda dasu kamo tare da gurfanar da wanda ake kara a duk idna yake, amma wannan umarnin na kan kwamishinan yansandan jihar Sakkwato ne ba shugaban yansandan Najeriya ba.”

Daga nan sai Alkai ya dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Afrilu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel