Abunda na rubuta gaskiya ne, babu wanda ke bina bashi – El-Rufai

Abunda na rubuta gaskiya ne, babu wanda ke bina bashi – El-Rufai

- Nasir El-Rufai ya nace kan cewa babu hakurin da zai bayar game da wasikar sa ga shugaban kasa

- A wata hira da akayi da shi kwanan nan, ya nace kan cewa lallai dukkan abubuwan da ya rubuta gaskiya ne kuma yana nan akan bakar sa

- Gwamnan na jihar Kaduna ya kuma bayyana cewa wannan ba shine wasikar san a farko ko na karshe ga fadar shugaban kasa ba

Abunda na rubuta gaskiya ne, babu wanda ke bina bashi – El-Rufai

El-Rufai ya bayyana cewa yana nan a kan bakarsa game da wasikar da ya aike ma shugaba Buhari

A lokacin da Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya rubuta wata wasika ga shugaban kasa Buhari inda ya soki wasu mutane dake kewaye da shugaban kasa, mutane da dama sunyi mamakin zafin wasikar.

KU KARANTA KUMA: YANZU-YANZU: Yan ta'adda sun kai hari a wani gidan rawa

Don haka El-Rufai, ya nace kan cewa babu mai binsa bashin hakuri game da wasikar da ya rubuta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya bada shawaran cewa anyi wasu gyara.

A cikin wasikar, El-Rufai ya kafa hujja da shugaban ma’aikata na shugaban kasa, Abba Kyari da kuma babban sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, cewa mutanen dake kewaye da Buhari na da san zuciya sannan kuma basu da sanin makamar aiki.

A halin da ake ciki, kwanan nan NAIJ.com ta ruwaito cewa El-Rufai ya bayyana cewa ya karfafa ma mabiyansa da su fada masa gaskiya a ko wani lokaci.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa babban barazana ga ko wani gwamnati sune masu neman alfarma.

KU KARANTA KUMA: Dalilai 4 da suka sa DSS ta dakatar da Magu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel