Majalisar dattawa ta gayyaci shugaban jami’ar ABU kan Melaye

Majalisar dattawa ta gayyaci shugaban jami’ar ABU kan Melaye

Majalisar dattawa ta shirya gayyatan hukumar jami’ar Ahmadu Bello (ABU) don share kurar dake sama kan muhawarar dake kewaye da takardan digiri na Sanata Dino Melaye.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yan majalisa masu rinjaye zasu gayyaci hukumar makarantar a makon nan don sun yi Karin bayani game da zargin da akeyi kan takardan shaidan kammala karatu na Melaye.

Majalisar dattawa ta gayyaci shugaban jami’ar ABU kan Melaye

Majalisar dattawa ta gayyaci shugaban jami’ar ABU kan Melaye

Jaridar ta bayyana wata majiya dake fadin cewa sammacin zai lafar da kurar da ta tashi.

KU KARANTA KUMA: Dalilai 4 da suka sa DSS ta dakatar da Magu

Majiyar ta ce: “Majalisar dattawa zata gayyaci hukumomin jami’oin da Dino Melaye yace ya yi. Musamman, majalisa zata gayyaci jami’ar Ahmadu Bello don lafar da muhawarar dake tashi. ABU zata bayyana gaskiya a wannan makon. Dukkan zarge-zargen shirme ne, ABU bazata ba kowa gurbin karatu ba da credit uku ba.”

A bangaren ta, jaridar Vanguard ta rahoto cewa shugaban jami’ar ABU Farfesa Ibrahim Garba zai gurfana a gaban majalisa a yau, 27 ga watan Maris.

NAIJ.com ta kawo cewa muhawara ta ci gaba a karshen mako lokacin da wani Abdussobur Salaam, wani da suka yi makaranta guda da Dino Melaye ya bayyana cewa ba mamaki Sanatan bai kammala Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ba. Abdussabur yace Melaye sam ba mutumin kirki bane tun a da.

KU KARANTA KUMA: YANZU-YANZU: Yan ta'adda sun kai hari a wani gidan rawa

Malam Abdussabur yayi makaranta guda watau A.B.U Zaria da Dino Melaye yanzu kuma yana aiki a Jami’ar harkar gona na garin Abeokuta (FUNAAB), yace abubuwan da Dino Melaye ya aikata a baya ne su ke bin sa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel