Lauyoyi 6 sun kalubalance Buhari a kotu kan ki maye gurbin Ocholi

Lauyoyi 6 sun kalubalance Buhari a kotu kan ki maye gurbin Ocholi

- Wasu lauyoyin Najeriya sun kai karan shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ki maye gurbin marigayi ministan kwadago da Ingantuwar aiki, James Ocholi

- Lauyoyin sun bukaci babban kotun tarayya ta umurni shugaban kasa ya nada wani minista ba tare da wani jinkiri ba

Lauyoyi 6 sun kalubalance Buhari a kotu kan ki maye gurbin Ocholi

Lauyoyi 6 sun kalubalance Buhari a kotu kan ki maye gurbin Ocholi

Wasu lauyoyin Najeriya 6 sun kai karan Shugaba Muhammadu Buhari a gaban kotu domin ki maye gurbin marigayi ministan kwadago da Ingantuwar aiki, James Ocholi (SAN). Lauyoyin sun hada da: Felix Okolo, Femi Victor Motojesi, Samuel Ogala, Dickson Enema, David Adegbe da Titilope Akerejola.

Lauyoyi sun kai karan shugaba Buhari domin ki nada sabuwar minista don cika gurbin marigayi tsohon ministan wanda ya sanya mutanen jihar Kogi ba tare da wakili a zartarwar gwamnatin tarayya.

Marigayi Mista James Ocholi, mai wakiltar jihar Kogi, dansa da kuma matarsa sun kasance a wata mumunar hatsarin mota a ranar Lahadi, 6 ga watan Maris, 2016 a hanyan Kaduna zuwa Abuja wanda ta yi sanadiyar mutuwarsu.

KU KARANTA KUMA: Bayan Hamid Ali, majalisar dattawa ta gayyaci wasu ministocin Buhari yan Arewa

Duk da haka, a cikin takadar karar mai lambar: FHC / LKJ / C / 08/2017 da loyoyin suka kai a babbar kotun tarayya, Lokoja a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris, sun roki kotun ta umarni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wani sabuwar minista ba tare da wani jinkiri ba. Sun kara da cewa rashin yi haka ta sabawa wa tsarin mulkin kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel