Yadda sojojin Najeriya suka daki wani mutun har lahira (BIDIYO)

Yadda sojojin Najeriya suka daki wani mutun har lahira (BIDIYO)

- Glory Fagbayibi tayi ikirarin cewa jami'an sojin Najeriya sun daki mijin ta har lahira

- Matar marigayin ta ce sojoji hudu sun kai ma mijinta hari inda sukayi mai dukan rashin imani

- Misis Fagbayi tace matar gidan su ce ta soma kai farmaki

Wata mata daga jihar Ogun ta bayyana cewa jami’an sojojin Najeriya sun daki mijinta har lahira.

Glory Fagbayibi ta fada ma manema labarai cewa sojojin guda hudu sun yi ma mijinta wani irin mugun duka kamar yadda mai gidansu dake 10 Prince Jamiu Oyebade, kusa da gurin wanke mota a Ogijo, jihar Ogun ta bukata.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nada wani dan Arewa shugaban babban banki

NAIJ.com ta tattaro cewa mijin Glory, wanda matar gidan da suke haya ke bi kudin haya na wata daya, ya mutu bayan kwanaki 15 da kai masa harin.

A nan kasa wani bidiyo ne da Sahara Reporters ta samo.

A halin da ake ciki, hukumar sojin Najeriya ta karyata wani rahotanni dake cewa rundunar bataliya 174 na Ikorodu sun kashe wani Mista George dake Ogijo, jihar Ogun.

A wata sanarwa daga daraktan hulda da jama’a na hukumar soji, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman, hukumar soji ta bayyana cewa wani Mista Kenny Abel Adesanya ne ya yada labarin marigayin da hoton a shafin san a twitter.

S.K Usman, ya bayyana cewa bincike ya tabbatar da cewa zargin karya ne, don haka Mista Adesanya ne ya shirya makircin sa, da tsanar sag a hukumar sojin Najeriya sannan yayi yunkurin janye hankalin mutane daga wadanda suka aikata wannan mumunan aiki.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel