Daga karshe, El-Rufai yayi fashin baki a kan wasikar da ya aike wa Buhari (Karanta)

Daga karshe, El-Rufai yayi fashin baki a kan wasikar da ya aike wa Buhari (Karanta)

- Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce bashi bane ya fitar da wasikar da ya rubuta wa Buhari

- El-Rufai ya fadi hakanne a wata hira da yayi da taridar Daily Trust na ranar Lahadi

Daga karshe, El-Rufai yayi fashin baki a kan wasikar da ya aike wa Buhari (Karanta)

Daga karshe, El-Rufai yayi fashin baki a kan wasikar da ya aike wa Buhari (Karanta)

A hirar yace wasikar sa yayi ta ne tsakaninsa da Buhari bai taba tunanin ya bari duniya ta sani ba, kuma da ya so hakan da tuntuni ya fitar amma bai yi ba.

El-Rufai yace wasu ne kawai da suke adawa da shi saboda matukar soyayya da yake nuna wa Buhari ke yi masa zagon kasa.

KU KARANTA: Najeriya na tafka mummunar asara - Pantami

“Ba ni bane na fitar da wasikar ba kuma idan har nine babu abinda zai hana ni fadin haka, amma ina son kowa ya sani yau cewa bani bane na fitar da wasikar da na rubuta wa Buhari kuma har yanzu ina kokarin gano dalilin da yasa wadanda suka fitar sukayi hakan ganin cewa wasikar ba na yi ta bane domin idanun duniya, tsakanina ne da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

“Ina ganin na rubuta wa Buhari wasiku da suka kai sama da goma tun daga lokacin da na sanshi zuwa yanzu kuma dukkansu sai naga wani abu da yake neman a gyara wanda shi bai ankare ba sai in rubuta domin sanar masa.''

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel