Ndume ya ce baya gaba da Saraki ko Dino Melaye

Ndume ya ce baya gaba da Saraki ko Dino Melaye

Sanata Dino Melaye ya musanta maganan cewa yana gaba da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Sanata Dino Melaye, saboda ya bukaci a bincikesu

Bana sa’insa da Saraki ko Dino Melaye – Ndume

Bana sa’insa da Saraki ko Dino Melaye – Ndume

Tsohon shugaban masu rinjayen majalisan Sanata Ali Ndume, ya musanta cewa yana sa’insa da Bukola Saraki da Dino Melaye.

Gaba da cewan jaridar Daily Trust, kamata yayi yabe shi ba wai sukarsa, akan kawo maganan a majalisar dattawan Najeriya.

KU KARANTA: Buhari ya keta tarihi, ya saki Tiriliyan 1 domin aiki

Yace: “ Kana cewa kada inyi maganan ne? Fili na kowa ne, kuma yana cikin al’adan majalisa na 14 da 15. Akwai wadanda aka bincika kafin yanzu.

“An taba bincikar Masari, tsohon kakaki akan takardansa kuma an wanke sa. An bincike Bankole akan rashin yin bautan kasa kuma an bincikesa. Hakazalika Paticia Etteh, kuma ta wanke kanta.”

“A majalisar dattawa, Enwerem ya samu matsala a sunansa na ‘S’ a takardansa cewa ‘Evan ko Evans’ an bincikes kuma yayi murabus. An binciki Chuba Okadigbo kuma ya rasa kujerasa.”

An tuhumci Adolphus Wabara akansa rashawa kuma an bincikesa. Ko David Mark an tuhumcesa kuma anyi bincike an wankesa.”

Ali Ndume yace ba wai yayi hakan bane dan an tsigeshi a matsayin shuagban masu rinjaye a majalisar dattawa.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel