EFCC: Wane mataki Buhari zai yanke game da Magu

EFCC: Wane mataki Buhari zai yanke game da Magu

Majalisa dai ta rubutawa shugaban kasa game da kin amincewa da Ibrahim Magu da tayi a matsayin shugaban Hukumar EFCC kwanakin baya wanda wannan ne dai karo na biyu da aka yi hakan

EFCC: Wane mataki Buhari zai yanke game da Magu

Wane mataki Buhari zai dauka game da Magu?

Yanzu haka dai ya ragewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara aika sunan Magu ko kuma ya nemi wani dabam ya jagoranci Hukumar EFCC inji Ministan shari’a na kasar Abubakar Malami SAN.

Ministan yace kuma Ibrahim Magu zai cigaba da aiki a matsayin mukaddashin shugaban Hukumar EFCC duk da cewa Majalisa ta ki tabbatar da shi. Shi dai Minista Malami yace ya tura rahoton aikin sa ga shugaban kasa.

KU KARANTA: Ko ka san nawa Shugaba Buhari ya ba kowace Jiha?

EFCC: Wane mataki Buhari zai yanke game da Magu

Buhari kadai zai yanke shawara game da Magu Inji AGF

Hukumar DSS ta zargi Magu da wasu laifuffuka. Sai dai tun kwanaki a wata takarda da NAIJ.com ta samu, Ibrahim Magu ya aikawa Ministan shari’a na kasar takarda inda ya wanke kan sa daga wadannan zargi.

Yanzu haka dai shugaban kasa ne zai dauki mataki na karshe game da lamarin. Ko dama dai Majalisa tace ita ta gama aikin ta, ya rage ga shugaban kasa Buhari. Shi kuwa Magu yace zai yi bakin kokarin sa wajen yaki da sata a kasar a duk halin da ya samu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel