Sanata Dino Melaye na cikin tsaka-mai-wuya

Sanata Dino Melaye na cikin tsaka-mai-wuya

Jaridar nan ta Sahara Reporters ta fa tasa Sanata Dino Melaye a gaba inda bayyana cewa ashe Sanatan bai yi karatun da yake ikirari ba. Yanzu haka dai magana na kotu

Sanata Dino Melaye na cikin tsaka-mai-wuya

An fallasa Sanata Melaye: ashe bai yi karatu ba?

Kwanaki Jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa Sanata mai wakiltar gabashin Kogi Dino Melaye bai karasa karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ba. Kuma dai har yanzu Jami’ar ba ta fito da cikakken bayani game da lamarin ba.

Yanzu haka an dai gano cewa sunan Dino Melaye ba ya cikin shafin wadanda suka halarci makarantar a baya. Digirin Dino Melaye dai na nuna cewa ya kammala karatu ne a shekarar 2000 alhali yayi bautar kasa tun a shekarar 1999. Akwai ma jita-jitar cewa Dino Melaye ya taba satar talabijin lokacin yana shugaban Dalibai.

KU KARANTA: Ana nema a hana bara a Arewa

Sanata Dino Melaye na cikin tsaka-mai-wuya

Sanata Dino Melaye na cikin tsaka-mai-wuya

Kwalejin ilmin tattalin arziki na Landan dai tayi wuf tace ba ta taba yin wani Dalibi mai suna Dino Melaye ba. Yayin da Jami’ar Harvard tace Dino ya zo wani taro ne na ‘yan kwanaki kurum amma ba Digiri yayi ba kamar yadda yake fada ba.

Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa yanzu haka yana karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya inda yake Digirin sa na 7. Sai dai akwai alamar tambaya game da lamarin yanzu haka dai Majalisa da Gwamnatin tarayya ta fara bincike game da batun wanda na iya jefa Sanata Melaye cikin babbar matsala.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel