Ana kokarin hana bara da talla a Jihohin Arewa

Ana kokarin hana bara da talla a Jihohin Arewa

Wata Kungiya mai suna YouthHubAfrica na kokarin ganin an kawo karshen matsalolin da ake samu a Arewacin kasar nan

Ana kokarin hana bara da talla a Jihohin Arewa

Taron Jama'a wajen taron a Kaduna

Wata kungiya mai suna YouthHubAfrica na kokarin ganin yadda za a kawo karshen cin zarafin kananan yara da ake yi a kasar nan musamman a Arewacin Najeriya. Don haka ne ma dai aka shirya wani taro na karawa juna sani na kwanaki 3 a Garin Kaduna wanda NAIJ.com ta samu halarta.

‘Yan Jarida da sauran ma’aikata masu ruwa da tsaki daga Jihohin Kaduna, Kano, Sokoto, Kebbi har ma da Jihar Oyo su ka halarci taron. Ana dai kokarin ganin yadda Majalisun Jihohi za su kafa wannan dokar nan da ta kare hakkin kananan yarada kuma dabbaka ta.

KU KARANTA: An kama Lauyan karya a Kano

Ana kokarin hana bara da talla a Jihohin Arewa

Rotimi Olawale a lokacin taron

Dokar za ta ba ‘ya ‘ya ‘yancin su auri wanda su ke so idan har sun girma sannan kuma a ba su ilmi mai inganci tare da haramta masu talla da yawan bara wanda hakan ke haifar da ‘da mara ido a al’umma.

An dai gayyaci manyan mutane inda suka gabatar da lacca da kasida game da batun. A mafi yawan Jihohin Arewa dai ba a kafa wannan doka da za ta ba yara ‘yancin su ba. Wanda ba shakka wannan na cikin abubuwan da ke maido mu baya kamar yadda Mawaki ya fada:

“Matukar yayan mu suna bara,

Titi da Loko-lokon Nijeriya.

Hanyar birni da na kauyuka,

Allah baku mu samu abin miya.

Sun yafu da fatar bunsuru,

Babu mai tanyonsu da dukiya…

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel