Buhari zai ziyarci Dajin Sambisa a Borno

Buhari zai ziyarci Dajin Sambisa a Borno

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci dajin Sambisa da ya kasance tsohon babban sansanin mayakan Boko Haram a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Buhari zai ziyarci Dajin Sambisa a Borno

Buhari zai ziyarci Dajin Sambisa

Buhari zai kai ziyarce a ranar Litinin don kaddamar da gasar nuna kwarewar sarrafa kananan makamai tsakanin sojojin kasar ta wannan shekarar.

Ministan tsaro na kasar, Alhaji Mansur Dan Ali da kuma manyan hafsoshin soji na cikin wadanda za su yi wa shugaba Buhari rakiya zuwa dajin na Sambisa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya tsige wani babban sakateren

A cikin watan Disamban bara ne dai, dakarun Najeriya suka yi nasarar fatattakar ‘yan Boko Haram daga Dajin.

NAIJ.com ta rahoto cewa, sojojin za su yi amfani da wannn gasar wajen gudanar da wasu ayyuka da suka hada da isar da magunguna ga 'yan gudun hijira da ke zaune a sansanonin Bama da Konduga da Magumeri da ke jihar ta Borno.

Kazalika dakarun za su raba kayayyakin jin-kai ga 'yan gudun hijirar kafin daga bisani su gana da sarakunan gargajiya don tattaunawa kan sha'anin tsaro.

KU KARANTA KUMA: Wayyo! Ana nema a kashe ni Inji Hadiza Bala Usman

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel