Yadda muka gano dukiyoyin Alex Badeh – EFCC

Yadda muka gano dukiyoyin Alex Badeh – EFCC

Wani shaida ya bayyana yadda hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gano dukiyoyin da tsohon babban hafsan tarayya, Air Chief Marshal Alex Badeh.

Yadda muka gano dukiyoyin Alex Badeh – EFCC

Yadda muka gano dukiyoyin Alex Badeh – EFCC

An gurfanar da Badeh akan laifuka 10 na almundahana da satan kudi sama da N3bn ta hanyar wani kamfani nashi Iyalikam Nigeria Ltd.

Nuhu Buhari, wani ma’aikacin EFCC yace hukumar ta nadashi a matsayin wanda zai shugabanci binciken dukiyoyin Alex Badeh.

KU KARANTA: Rikicin jam'iyyar PDP bata kare ba

A gaban Lauyan EFCC Rotimi Jacobs, Nuhu ya lissafa dukiyoyin wanda ya kunshi gidaje masu lamba 19 Kumasi Crescent, Wuse 2; No 6 Ogun River, Maitama, Abuja; No 2 Nelson Mandela Street, Asokoro; No 2 Oda Crescent off Addis Ababa Street, Wuse 2 da kuma babban shago.

Da aka je daya daga cikin gidajen, an ga yaronshi a ciki amma ya musanta cewa shi haya yakeyi. Yace gidan wani Oluwatoyin Nike ne kuma ta sayarwa Mohammed Umar da Kair Sardau a kudi N260 million.

Da aka tuntubi Sardau, ya amince da cewa ya sayi gidan amma a madadin yaron Alez Badeh ta hanayr wani Air Commodore S.A Yusha’u.

Jastis Okon Abang ya dakatad da karan zuwa ranan 2 ga watan Mayu dominn cigaba.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel