Sanata Makarfi yace rikicn jam'iyyar bata kare ba

Sanata Makarfi yace rikicn jam'iyyar bata kare ba

- Bangaren Ahmed Makarfi na jam’iyyar PDP sunce har yanzu basu gama rikici da bangaren Ali Modu Sherrif ba

- Yace sulhun da akayi kawai na zaman lafiya ne ba sulhun rikicin jam’iyyar ba

- Tace har yanzu tana sauraron hukuncin da kotun koli zata yanke akan zancen

Da sauran baraka a PDP, bamu gama dinketa ba – Makarfi

Da sauran baraka a PDP, bamu gama dinketa ba – Makarfi

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta musanta rahoton cewa bangaren Ahmed Makarfi da kotu sun amince da Ali Modu Sherrif a matsayin shugaba.

A wata jawabin da ta saki a yau Juma’a, 24 ga watan Maris kuma mai magana da yawun jam’iyyar, Prince Dayo Adeyeye, ya rattaba hannu, yace har yanzu ba’a dinke barakan da ke tsakaninsu ba.

KU KARANTA: Hakan mai a arewa ta samu wani cikas

Sashen Jawabin tace: “An jawo hankalin kwamitin rikon kwarya karkashn jagorancin Ahmed Makarfi akan wasu wallafe-wallafe da akeyi a jaridu na cewa jam’iyyar PDP ta dinke barakan da ke tsakaninta.”

Wannan ba gaskiya bane kuma muna son fada muku cewa yarjejeniyar da akayi jiya gaban gwamnan jihar Bayelsa kawai domin takaita barakar jam’iyyar ne da kafafen yada labarai keyi da kuma soke-soken masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.

“Ku sani cewa, yarjejeniyar da mukayi bata sulhu bane, kawai munyi ne domin jawo hankalin yan jam’iyyar wajen hada kansu domin kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC a shekarar 2019.”

NAIJ.com tana tuna muku cewa an samu rahotanni a ranan Alhamis, 23 ga watan Maris cewa anyi ulhu tsakannin Ali Modu Sherrif da Ahmed Makarfi domin dinke barakan da ke cikin jam’iyyar.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel