Shugaban kasa ya aika takarda ga kasar Birtaniyya

Shugaban kasa ya aika takarda ga kasar Birtaniyya

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wasika ga shugaban kasa Birtaniyya Theresa May inda yake mika godiyar Najeriya wajen yaki da ta’addanci da kasar ta taimaka kwarai

Shugaban kasa ya aika takarda ga kasar Birtaniyya

Shugaba Buhari ya aika takarda ga kasar Birtaniyya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika takarda ga Firayim Ministar kasar Birtaniya inda yake mata godiya game da yadda aka taimakawa Najeriya wajen yaki da ‘yan ta’addan Kungiyar Boko Haram.

Shugaba Buhari ya godewa Kasar Birtaniya ne saboda irin kokarin da suka yi na taimakawa Najeriya da mukamai da kayan aiki wajen yakar Boko Haram. Mai magana da bakin shugaban kasar Femi Adesina ne ya bayyana haka a Yau Juma’a.

KU KARANTA: Rikicin Majalisa da shugaban kasa yayi kamari

Shugaban kasa ya aika takarda ga kasar Birtaniyya

Buhari ya aika takarda ga kasar Birtaniyya

Shugaba Buhari ya aika takarda ga Theresa May inda yace a madadin sauran mutanen Najeriya suna godiya ga yadda aka taimakawa kasar. Shugaban kasar ya kuma yi tir da harin da aka kai a Landan kwanan nan.

Haka kuma Femi Falana SAN wanda shararren Lauya ne a Najeriya ya bayyana cewa Majalisar dattawa na da damar bada umarni a kama Sakataren Gwamnatin kasar Babachir David Lawa. Falana yace doka ta na Sanatocin wannan damar idan har Babachir bai hallara gaban ta ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel