Rundunar mayaƙan sojan ƙasa zata fara gasar sarrafa makamai a dajin Sambisa

Rundunar mayaƙan sojan ƙasa zata fara gasar sarrafa makamai a dajin Sambisa

Rundunar mayakan sojan kasa sun tabbatar da fara amfani da dajin Sambisa don gasar sarrafa kananan makamai da zai gudana a shekarar 2017, kamar yadda NAIJ.com ta samu rahoto.

Rundunar mayaƙan sojan ƙasa zata fara gasar sarrafa makamai a dajin Sambisa

Shugaba Buhari

Shugaban tsare tsaren atisaye na rundunar sojin Manjo janar David Ahmadu ne ya sanar da haka inda yace duk da samun galaba da rundunar ta samu akan kungiyar Boko Haram, da kuma kwato dajin Sambisa, rundunar ta samar da ingantaccen tsarin samar da tsaro a dajin yayin gudanar da gasar.

Ahmadu yace kimanin nisan kilomita 20 da za’a yi amfani da shi wajen gudanar da gasar, an shinge sa, kuma an karfafa tsaro a yankin don gudun duk wani harin Boko Haram.

KU KARANTA: Rotsi! Jami'in hanya ya lakaɗa ma Fasto ɗan banzan duka a Zamfara, kalli yadda suka dambace

Rundunar mayaƙan sojan ƙasa zata fara gasar sarrafa makamai a dajin Sambisa

Rundunar mayaƙan sojan ƙasa

Ahmadu ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai, inda yace za’a fara gasar a ranar Litinin zuwa Juma’a, yace manufar shirya gasar itace don tabbatar da tsaron dajin Sambisa musamman don gudanar da harkokin rundunar sojin kasar nan.

Sa'annan yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ne mai masuakin baki, kuma zai samu rakiyar babban hafsan soja Janar Olanisakin, ministan tsaro Mansur Dan- Ali tare da babban hafsan sojan kasanJanar Tukur Buratai, da sauran manyan hafsoshin soji.

Rundunar mayaƙan sojan ƙasa zata fara gasar sarrafa makamai a dajin Sambisa

Sojoji a dajin Sambisa

Yace a kwanan baya ne injiniyoyin soji suka fara gina kwalbatoci da tituna don sawwaka shiga da fita dajin Sambisa, Manjo David yace za’a yi amfani da makamai daban daban a yayin gasar, sa’annan kuma zasu gudanar da ayyukan sa kai kamar su wayar da kawunan mutane kan lamurran tsaro, da kuma tallafa ma yan gudun hijira.

Daga karshe David yace gasar rawan dajin zai sanya jami’an soji kwarewa akan iya harbi da kuma kara musu horo kan yadda zasu tsare kasar gaba daya.

A wani labarin kuma, kaakakin rundunar sojin kasa Birgediya SK Usman yace sojojin bataliya ta 103 tare da hadin kan sojojin sa kai, wato Sibiliyan JTF sun kakkabe yan Boko Haram daga kauyen Gombole dake karamar hukumar Konduga, inda suka hallaka yan Boko Haram da dama.

“Sojojin sun gano bamabamai da kuma rusa kamfanin hada bamabamai a kauyen, sa’annan sun gano babura guda 3, rigunan kunan bakin wake, guda 4, kayan sojoji 4, tare da ceto yan mata 4 da yara 6.” Inji SK Usman.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel