Yan sanda sun ceto wata mata da ke kokarin hallaka kanta ta hanyar fadawa tekun Legas

Yan sanda sun ceto wata mata da ke kokarin hallaka kanta ta hanyar fadawa tekun Legas

Yayinda labarai suka yadu akan wani likita da ya hallaka kansa, Dr Allwell Orji, lokacin da ya fada cikin tekun Legas, jami’an yan sandan sun ceto wata mata da ke kokarin kwaikwayan abinda likitan yayi.

YANZU-YANZU : Yan sanda sun ceto wata mata da ke kokarin hallaka kanta ta hanyar fadawa tekun Legas

YANZU-YANZU : Yan sanda sun ceto wata mata da ke kokarin hallaka kanta ta hanyar fadawa tekun Legas

Matan tayi wannan abin takaicin ne a yau Juma’a, 24 ga watan Maris, 2017.

Game da cewar jaridar PM News, hukumar yan sandan jihar Legas ta ceto wata mata mai suna, Taiwo Titilayo Momoh wacce tayi kokarin hallaka kanta ta hanyar fadawa tekun Legas.

KU KARANTA: Majalisar dattawa ta fara kunnawa AGF Malami wuta

Kwamishanan yan sandan jihar Legas, Fatai Owoseni, ya bayyana cewa Momoh na hanyar Oworonshoki sai ta fadawa direban ya tsaya akan gadan.

Yace: “Tayi kokarin fadawa cikin tekun ne daga kan gadan Third mainland. Amma, an ceto ta. Tana cikin motan haya ne sai ta sauka akan gadan tayi kokarin fadawa.

“Sai yan sanda suka hangota da wuri suka ceceta kafin ta samu fadawa cikin tekun.”

Kwamishanan yace ta shiga cikin kunci ne kan basussukan da ake binta. Ko lokacin da yake magana da ita, ta rantse sai ta kashe kanta.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel