Wani kwararren dan siyasa ya tona babban asirin majalisar dattijai

Wani kwararren dan siyasa ya tona babban asirin majalisar dattijai

An bayyana cewar Sanatocin Tarayya Nijeriya sun ki yarjewa da kudirin da Shugaban Buhari ya kawo na tabbatar da baiwa Ibrahim Magu shugabancin Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Nijeriyan Zagon Kasa (EFCC) ne a bisa tsoron da suke yi na tonon sililin da ka iya biyo baya kan ayyukansu na boye.

Wani kwararren dan siyasa ya tona babban asirin Majalisar dattijai

Wani kwararren dan siyasa ya tona babban asirin Majalisar dattijai

Alhaji Bello Dan Malikin Lanzai ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakilinmu a Bauchi.

Dan Malikin ya bayyana takaicinsa da mamakinsa a bisa rashin amincewa da Ibrahim Magu da Sanatocin suka yi.

“Sanatoci su ne suka hana komai tafiya a kasar nan, su ne suka hana Buhari aiki a Nijeriya. Duk wani abun da zai shafi abun arziki wa talakawa to ba za su so ba; domin daman sune matsalar kasar nan. Galibinsu tsoffin gwamnoni ne wadanda suke da kashi a gidinsu. Tun da ake nada shugaban EFCC ba’a taba samun mai aikin Magu ba, don meye ba za a yarje masa ba”. in ji shi

KU KARANTA: An dakatar da basarake a Katsina

Ya ci gaba da cewa “Abin da suke tsoro ke nan idan Magu ya shiga wajen suna ganin asirinsu ya tonu, a sabili da haka za su dauru, za a zo ana fadin kudaden da suka boye a gidajensu. Duk wadannan abubuwan ta yaya za a yi su Bukola Saraki wanda ana shari’a a kansa ya yarda kuma da irin su Magu a hukumar EFCC? Ya riga ya san Magu zai daure shi”. In ji Lanzai

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel