Buhari ya nada mutanen da baya iya juyawa - Onigbinde

Buhari ya nada mutanen da baya iya juyawa - Onigbinde

Daya daga cikin shugabannin kungiyoyin fafutuka, BudgIT Nigeria, Seun Onigbinde yace shugaba Muhammadu Buhari ba shi da iko akan wadanda ya nada aiki.

Buhari ya nada mutanen da baya iya juyawa - Onigbinde

Buhari ya nada mutanen da baya iya juyawa - Onigbinde

Wasu daga cikin wadanda shugaba Buhari ya nada irinsu Babachir David Lawal yanada kashi a gindi.

A wata magana da yayita shafin Tuwitansa, Seun Onigbinde, yayi maganganu da dama domin bada hujja akan maganarsa.

KU KARANTA: An dakatad da wani basarake akan fyade

“Daga jawabin DSS akan Magu, sai kare Babachir, sai yarda da Hameed Ali, wannan na nuni da cewa Buhari ya nada mutanen da baya iya juyawa.”

An samu rahotanni da dadewa cewa akwai wasu kusoshi a gwamnatin Buhari masu juyashi, wasu kuma sunce yan tsiraru sun kwace gwamnatin.

A watan da ya gabata, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufai ya tabbatar da cewa akwai wasu kusoshi a fadar shugaban kasa, amma yace babu ruwanshi a ciki kuma baya cikinsu.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel