Dala na cigaba da shan kayi, yayin da darajan naira ya kai N385

Dala na cigaba da shan kayi, yayin da darajan naira ya kai N385

Masu hada hadan dalan Amurka sun cigaba da samun sauki yayin da ake siyar da dala daya akan naira N385, wanda hakan ya kawo ma yan canji tarnaki.

Dala na cigaba da shan kayi, yayin da darajan naira ya kai N385

Dala na cigaba da shan kayi, yayin da darajan naira ya kai N385

Yan kasuwa sun bayyana dalilin daya sanya dalar ke kara faduwa shine sakamakon cigaba da afka dalan Amurka a kasuwan canji da babban banki, CBN ke yi.

KU KARANTA: ‘Buhari yayi taka-tsantsan da yan amshin shata’ - inji Sarkin Kano

Naij.com ta gano ko a jiya sai da CBN ta antaya dala miliyan 100 a kasuwan canji, inda masu siya akan sari suka siya dalan miliyan 91.

Daraktan watsa labarai na CBN, Isaac Okafor ya bayyana cewa dilolin dala zasu samu riba zuwa ranar Juma’a 24 ga watan Maris, sa’annan ya tabbatar da cewa dalan Amurka zata kara faduwa zuwa N33, N320.

Zuwa yanzu dai naira ta samu tagomashi da kashi 25 a kasuwannin bayan fagge tun lokacin da babban bankin ta sanar da sabon tsarin canji a ranar 20 ga wata Feburairu, wanda kafin wannan lokacin ana siyar da dala guda akan N520.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel