Buhari ya tsige wani babban sakateren

Buhari ya tsige wani babban sakateren

- Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin tsige wani babban sakataren, wanda ake zargin awon gaba da wasu makudan kudi na ma’aikatar

- Jami’ai tsaro sun tabbattar cewa mutumin na amfani da kamfanonin fiye da 500 domin tafka wa gwamnatin tarayya zamba

Buhari ya tsige wani babban sakateren

Shugaba Buhari ya umurnin tsige wani babban sakateren.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin tsige wani babban sakataren, wanda ake zargin yin amfani da ofishinsa domin tafka wa gwamnatin tarayya zamba ta hanyar ba da kwangila mai daraja biliyoyin naira ga kansa.

Babban sakatare, wanda shugaba Buhari ya nada a shekara 2015, aka kora a ranar Talata, 21 ga watan Maris a kan umarni shugaban kasar.

Wata majiya a ma'aikatar tabbatar da cewa jami’an 'yan sanda 2 suka hawon gaba da babban sakatare daga sakatariya na tarayya da ke Abuja.

Wata majiya daga fadar shugaban kasar ta tabbatar wa Naij.com cewa shugaban kasar ya umarnin tsige babban sakataren.

Daya daga cikin jami’ai tsaro, masu gudanar da bincike na kori babban sakatare, ya shaida wa wakilinmu cewa makircin sakataren ya tilasta su da su jinkirta da kama shi tun watan Janairu na wannan shekara.

Jami’an ya ce sun saka idanu ga mutumin da kuma fiye da kamfanonin 500 daban-daban da ya ke amfani da su don awon gaba da makudan kudi daga ma'aikatar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel