To fa! Wata sabuwar barazana na shirin hana aikin hako fetir a Arewa

To fa! Wata sabuwar barazana na shirin hana aikin hako fetir a Arewa

Watanni uku bayan komawa bakin aiki bincken albarkatun man fetur a iyakokin jihohin Bauchi da Gombe, Kamfanin kasar China da ke gudanar da aikin na fuskantar bore da fushin al'umma da ke yankin, inda suke neman a biya su diyyar filayeda gonakinsu da aikin ya ci.

To fa! Wata sabuwar barazana na shirin hana aikin hako fetir a Arewa

To fa! Wata sabuwar barazana na shirin hana aikin hako fetir a Arewa

A makon jiya ne dai jaridar NAIJ.com ta ruwaito maku cewa Sama da shekaru ashirin 20 ne masana suka tabbatar da cewar kauyen Baranbo dake Karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi akwai danyen man fetur malale a wajen, wanda Allah Ya azurta Nijeriya da shi. A bisa haka ne Ma’aikatar Man Fetir ta kasa, NNPC ta kudiri aniyar hako danye man da kuma binciken man a wannan kauyen inda aka fara aikin a watannin baya.

KU KARANTA: Elrufa'i na yin wata muhimmiyar ganawa da Osinbajo

Da yake nasa jawabin, Shugaban Hukumar Mai ta Kasa NNPC, Maikanti Baru ya bayyana cewar sun yi wa aikin shiri na musamman wanda sun kawo na’o’iri da manyan kayan aiki don ganin sun kai ga samo man fetur din.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Babban Manajan Gamayya na Frontier Ddploration Serbices, Dakta Mazadu Bako ya ci gaba da cewa Nijeriya za ta ci moriyar aikin fiye da yanda ake tsammani.

A cewar ta hukumar ta NNPC, nan da wata uku za mu fitar da sakamakon aikin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel