An dakatar da wani Basarake saboda fyade

An dakatar da wani Basarake saboda fyade

Fadar masarautar Katsina ta dakatar da Bashir Bala Kofar-bai daga mukaminsa na 'Magatakarda' saboda zargin aikata laifin fyade da ake yi masa.

Sakataren Majalisar masarautar, Bello Ifo, ya fada a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 23 ga watan Maris, cewa dakatarwar ta fara aiki ne nan take.

An dakatar da wani Basarake saboda fyade

An dakatar da wani Basarake saboda fyade

Bashir Bala na fuskantar shari'ar aikata laifin fyade ga wata yarinya 'yar shekara 15 makonni biyu da suka gabata a Katsina.

KU KARANTA KUMA: Wani babban Sarki a Arewa ya rasu

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa ana zargin Basaraken ne da yi wa yarinyar fyade, bayan da mahaifinta wanda ke aiki a karkashin Basaraken ya aiketa gidansa.

Yarinyar ta sanar da iyayenta halin da take ciki, inda suka dauke ta zuwa asibiti domin duba lafiyarta.

Daga nan kuma iyayen suka sanar da 'yan sanda, inda aka kama shi tare da tsare shi domin gudanar da bincike.

Hadin gwiwar kungiyoyin fararen hula a Jahar dai, na kara matsa wa 'yan sanda lamba, da su tabbatar da adalci a kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa na shirin dakatar da Gwamnatin Buhari?

Batun aikata fyade ga kananan yara na ci gaba da addabar al'umma musamman a arewacin Najeriya.

A lokuta da dama akan zargi hukumomi da kasa yin katabus wurin hukunta wadanda ake zargi.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel