‘Buhari yayi taka-tsantsan da yan amshin shata’ - inji Sarkin Kano

‘Buhari yayi taka-tsantsan da yan amshin shata’ - inji Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi taka tsantsan da fadawansa na fadar gwamnati, don kuwa tamkar masu amshin shata suke.

‘Buhari yayi taka-tsantsan da yan amshin shata’ - inji Sarkin Kano

‘Buhari

Sarkin yayi wannan gargadi ne a ranar Alhamis 23 ga watan Maris a taron tunawa da babban lauyan Kehinde Sofola a jihar Legas, inda yace yan amshin shata sune asalin makiyan shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma idan bai bi a hankali dasu ba, zasu lalata duk wani kokarin dayake yi.

Sarki ya shawarci Buhari da kada ya dinga kyamar masu sukar gwamnatinsa “Ina tausayin masu rike da madafan iko, saboda a koda yaushe zagaye suke da makiya”, Sarki yace ya shugaba Buhari na bukatan mutanen da zasu dinga fada masa gaskiya komai dacinta.

KU KARANTA: Ciwon hauka ya samu wata mata, yayin da gwamna Ambode ya rusa mata gida

Sunusi yace dalilin daya sa ya fallasa badakalar sama da dala biliyan 20 a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck shine saboda baya tsoron barin kujerarsa, saboda ya san ba zai dawwama a kujerar dindindin ba.

‘Buhari yayi taka-tsantsan da yan amshin shata’ - inji Sarkin Kano

Sarkin Kano

Sarki yace wasu mutane suna tsoron fada ma shuwagabanni gaskiya ne saboda gudun kada a sallame su daga aiki, “duk mutanen da ake tsoron fada ma gaskiya suna ina ne yanzu? Don haka wadanda suke kan mulki suma su tuna mulki mai wucewa ne.” inji shi

Mai martaba ya cigaba da fadin cewa baya ruduwa idan fadawa suna fada masa cewa zai dawwama a kan mulki, don haka ne ma baya tuntubarsu dangane da muhimman shawarwari, sa’annan dalilin daya sa ya daina sukar shugaba Jonathan shine saboda ya bar mulki, don kuwa idan na kan mulki ne zaka fada masa gaskiya. “idan kana son zama dan kasa na gari, toh ka fada ma gwamnati mai ci gaskiya”.

Dayake bada labarin yadda ya bar kujeran gwamnan CBN, Sunusi yace “Dole dai wata rana in bar kujerar gwamnan CBN, zan iya mutuwa, wa’adin mulki na ka iya karewa, ko kuma a tsige ni, bani da iko kan wannan. Don haka ban yi mamakin sallama tab a, na san a rina, saboda an taba umarta ta da inyi murabus, amma naki ya.

“Amsa daya na basu, kace in yi murabus saboda na fada maka an saci kudi, sai dai ka fara fada ma ministan tayi ritaya.

“Mutane sun manta cewa wannan gwamnan ko shugaban kasa da kake jin tsoron fada ma gaskiya zai bar kujerarsa wata rana, abinda kawai za’a iya tunaka da shi a kai, shine yadda ka tafiyar da rayuwarka a lokacin da kake raye.” Inji Sarki

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel