‘Tsohon shugaban hafsan ya saci naira miliyan 800 ya gina shago’ – inji EFCC

‘Tsohon shugaban hafsan ya saci naira miliyan 800 ya gina shago’ – inji EFCC

Wani shaida daya gurfana a kotun dangane da shari’ar tsohon shugaban hafsan soji Alex Badeh, ya shaida ma kotu yadda Badeh ya kwashi kudin hukumar soji ya gina wani katafaren shago.

‘Tsohon shugaban hafsan ya saci naira miliyan 800 ya gina shago’ – inji EFCC

Hukumar EFCC ta zargi tsohon shugaban hafsan da satan naira miliyan 800

Shaidan mai suna Nuhu Dalhatu ya bayyana haka ne a gaban alkalin babban kotun birnin tarayya wanda ke sauraron karar da hukumae EFCC ta shigar da Alex Badeh kan tuhumarsa da take yi da aikata laifuka 10 da suka danganci satar kudi, cin amana da aikata almundahana har na zunzurutun kudi naira biliyan 3.79 a gabansa.

KU KARANTA: Kasar Japan ta samar ma al’ummar jihar Kebbi ruwan sha bayan kwashe shekaru 300 basu da ruwa

Yayin da lauyan EFCC Rotimi Jacobs ke yi ma Nuhu Dalhatu tambayoyi, wanda jami’i n bincike ne a EFCC, ya shaida ma kotu cewar sun gudanar da bincike kuma sun gano wasu kadarori da dama mallakin Alex Badeh, ciki har da katafaren shago mai adireshi lamba 2, Oda Crescent.

‘Tsohon shugaban hafsan ya saci naira miliyan 800 ya gina shago’ – inji EFCC

Katafaren shagon Badeh

“An umarce ni da in binciki badakalar kudin makamai data faro daga ofishin mashawarcin shugaban kasa kan lamurran tsaro, da kuma tsarin cinikayya na rundunar sojan sama. An bani daman binciken kadarori guda 5, da masu adireshi kamar haka: 9, Kumasi Crescent, Wuse 2; 6, Ogun River, Maitama; 2, Nelson Mandela Street, Asokoro; 2, Oda Crescent daura da Adis Ababa Crescent, Wuse 2 da kuam wani rukunin shaguna dake Ahmadu Bello, Garki 2” inji Nuhu Dalhatu."

Nuhu Dalhatu wanda shine shaida na 17 ya bayyana ma kotu cewar wannan gida dake 19, Kumasi Crescent na yaron Alex Badeh ne, yace da suka gayyaci yaron don amsa tambayoyi, sun gano daga bayanan daya basu cewa an siya gidan akan kudi naira miliyan 260 ta hannun wani tsohon daraktan kudi na hukumar sojan sama.

“Haka zalika mun gano cewar gida mai lamba 2 Oda Crescent, rukunin shaguna ne hawa 5, kuma ba’a kammala gina shi ba” inji shi

Nuhu Dalhatu ta cigaba da cewa “Har sai da muka gayyaci kamfanin dake gudanar da aikin ginin (Rytebuilders Technologies Limited), muka bukaci su nuna mana asusun tara kudaden su, da muka bincika sai muka gano wani asusun bankin Zenith mallakin kamfanin dauke da kudi naira miliyan 800, cikin riban da suka samu na naira biliyan 1.2, duk kudin hukumar sojin sama ne da aka ciro daga asusun su mai lamba NAF106B da kuma NAF Camp Accounts daga barikin Mogadishu, kuma wani E.A Abu da wani hafsan soja Seyi suka sa hannu wajen fitar da kudin.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel