‘Zamu ƙaddamar da ruwan Zaria nan bada daɗewa ba’ – gwamna El-Rufai

‘Zamu ƙaddamar da ruwan Zaria nan bada daɗewa ba’ – gwamna El-Rufai

A ranar 27 ga watan Mayu mai zuwa ne ake sa ran kaddamar da aikin ruwan Zaria wanda zai samar da lita miliyan 50 na ruwa a duka rana, inji gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai.

‘Zamu ƙaddamar da ruwan Zaria nan bada daɗewa ba’ – gwamna El-Rufai

Gwamna El-Rufai

Yayin da yake jawabi jim kadan bayan kammala zagayen duba aikin ruwan dake Zaria, Malam Nasiru El-Rufai ya yaba da matsayin da aikin ya kai, inda ya tabbatar da kammala aikin gaba daya a watan Afrilun shekara mai zuwa.

KU KARANTA: Hotunan wata makarantar Firamari a Kaduna dake da ɗalibai 300, kujeru 15 kacal!

‘Zamu ƙaddamar da ruwan Zaria nan bada daɗewa ba’ – gwamna El-Rufai

Gidan ruwa

Gwamnan ya bayyana cewa matsalar rashin ruwan sha a Zaria ya kusan zama tarihi. Gwamnan yace jama’an Zaria zasu fara ganin cigaba dangane da samun ruwan sha, inda sauran kananan hukumomi dake kewaye da Zaria zasu biyi sahu zuwa sabuwar shekara.

Gwamnan ya tabbatar da cewa aikin ruwan zai kammalu a iya daidai kudin da aka bayar da kwangilarsa, naira biliyan 69. A cewar gwamnan “Mun gamsu da aikin, mun gamsu da yadda ake gudanar da aikin gine ginen tankunan ruwa, bututun ruwa da duk sauran bangarorin aikin.

‘Zamu ƙaddamar da ruwan Zaria nan bada daɗewa ba’ – gwamna El-Rufai

‘Zamu ƙaddamar da ruwan Zaria nan bada daɗewa ba’ – gwamna El-Rufai

“Da ikon Allah zuwa ranar 27 ga watan Mayu na 2017 zamu kaddamar da aikin sashin da zai dinga ba jama’an Zari ruwa lita miliyan 50 a duk rana, mun sanya ranar ne don bikin cikar gwamnatinmu shekaru 2 akan mulki, kuma sauran kananan hukumomin dake kewaye da Zaria zasu biyu sahu zuwa watan Afrilun 2018.”

Gwamnan ya karkare jawabinsa da cewa “Zuwa wannan lokaci za’a kammala duk tankunan ruwan, mun tattauna da dan kwangilar, duk sun tabbatar mana da kammala aikin cikin lokaci.”

Ga sauran hotunan nan:

‘Zamu ƙaddamar da ruwan Zaria nan bada daɗewa ba’ – gwamna El-Rufai

Gwamna El-Rufai a yayinda yake duba ingancin aikin da gwamnatin sa keyi na samar da ruwa a Zari'a

‘Zamu ƙaddamar da ruwan Zaria nan bada daɗewa ba’ – gwamna El-Rufai

El-Rufai da mutanen sa yayinda suke duba yadda aiki ke gudana

‘Zamu ƙaddamar da ruwan Zaria nan bada daɗewa ba’ – gwamna El-Rufai

Gwamnatin Kaduna na ci gaba da aiki

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel