Ciwon hauka ya samu wata mata, yayin da gwamna Ambode ya rusa mata gida

Ciwon hauka ya samu wata mata, yayin da gwamna Ambode ya rusa mata gida

Wata mata a jihar Legas ta samu tabin hankali yayin da ma’aikatar gidaje ta rusa mata gidanta a yankin masulta, Otodo-Gbame na jihar Legas.

Ciwon hauka ya samu wata mata, yayin da gwamna Ambode ya rusa mata gida

Mahaukaciya

NAIJ.com ta gano daruruwan jama’an yankin sun shiga halin tsaka mai wuya bayan da gwamnatin jihar ta turo da jami’an tsaro dauke da muggan makamai wadanda suka mamaye unguwar don su fatattaki mazauna unguwar duk a cikin shirin rushe yankin.

KU KARANTA: An kammala shirin gina ma talakawa gidaje 180,000 kyauta a Najeriya - Daraktan ANDP

Sai dai dayawa daga cikin kungiyoyin kare hakkin biladama sun soki lamirin gwamnati na rusa gidajen mutanen, musamman yadda suka ce wata kotu ta dakatar da rushe rushe har sai ta kammala yanke hukunci bisa karar da aka shigar da gwamnatin gabanta.

Ciwon hauka ya samu wata mata, yayin da gwamna Ambode ya rusa mata gida

Matar

Amma duk da haka gwamnatin tayi kunnen uwar shegu da umarnin kotun, inda ta sanya aka rushe sama da gidaje 4000 a ranar Juma’a 17 ga watan Maris. Wasu mazauna yankin sunce basu da wata masaniya dangane da shirin rusau din “Mun yi mamaki matuka, bamu san daga inda suka fito ba, sai dai kawai muka ga suna rushe gidaje” inji Paul Kunmu

Tun a watan Nuwambar 2016 ne jama’a suka fara tashi daga yankin, inda sama da mutum 30,000 sunyi kaura daga unguwar.

Ga dai bidiyon matar nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel