Rundunar soji ta halaka ma’aikatar bam na Boko Haram a Borno

Rundunar soji ta halaka ma’aikatar bam na Boko Haram a Borno

Rundunar sojin Najeriya kan Operation Lafiya Dole sun gano wani ma’aikata na hada bama bamai a jihar Borno.

A cewar wata sanarwa daga kakakin hukumar soji, Birgediya-Janar Sani Kukasheka Usman, yace an gudanar da aikin ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Wani babban Sarki a Arewa ya rasu

NAIJ.com ta samu labarin cewa rundunar tare da wasu yan bangan Civilian Joint Task Force (CJTF) sun halaka ma’aikatar bam din bayan sun yi arangama da wasu yan kungiyar Boko Haram.

Kakakin sojin ya kara da cewa wani soja ya ji rauni a yayinda suke musayar wuta sannan hukumar sojin sama ta dauke shi don basa kulawa.

Karanta sanarwan a kasa:

Rundunar bataliya 103, sashi 7, na Operation LAFIYA DOLE tare da wasu yan bangan JTF a yau sunyi wani aikin kakkaba a Gombole, karamar hukumar Konduga dake jihar Borno.

A lokacin aikin, rundunar sun kau da wasu yan ta’addan Boko Haram da suka boye a yankin. Sannan kuma sun gano gurin hada bama bamai sann suka halaka gurin wanda ke a kauyen.

KU KARANTA KUMA: DA DUMI-DUMI: Shugaba Buhari yayi sabon nadi

Tawagar sun kuma samo Babura guda 3, rigar bam 4 da kuma kayan sojoji 4 da aka sace. Sun ceto mata 4 da yara 6 daga hannun yan ta’addan.

Abun bakin ciki, wani soja ya ji rauni sannan kuma hukumar sojin sama ta dauke shi. Sojan na samun lafiya.

Kalli hotuna a kasa:

Rundunar soji ta halaka ma’aikatar bam na Boko Haram a Borno

Mata da yara da rundunar ta ceto

Rundunar soji ta halaka ma’aikatar bam na Boko Haram a Borno

Kayayyakin da aka samo daga yan ta'addan

NAIJ.com ta kai ziyara ga yaran da suka tsira daga rikicin Boko Haram da kuma yadda suke rayuwa a sabon muhallin su.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel