Majalisar Dattawa na shirin dakatar da Gwamnatin Buhari?

Majalisar Dattawa na shirin dakatar da Gwamnatin Buhari?

Sanatocin Najeriya sun bayyana cewa ba su da wani shiri na dakatar da Gwamnatin shugaba Buhari. Mai magana da bakin Majalisar ya bayyana haka da kan sa

Majalisar Dattawa na shirin dakatar da Gwamnatin Buhari?

Ba mu da niyyar dakatar da Gwamnatin Buhari-Sanatoci

Sanata Aliyu Sabi Abdullahi Mai magana da bakin Majalisar Dattawa ya bayyana cewa Majalisa ba ta taba cewa za ta dakatar da aikin Gwamnatin tarayya da shugaba Muhammadu Buhari yake jagoranta ba.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Sanatoci sun bayyana cewa za su nemi su dakatar da Gwamnatin tun da dai har Sakataren Gwamnatin Tarayya Mista Babachir David Lawal ba zai bayyana a gaban Majalisa domin bincike ba.

KU KARANTA: Sanatoci 7 da suka nemi a tsige Hamid Ali

Majalisar Dattawa na shirin dakatar da Gwamnatin Buhari?

Sanatoci sun karyata maganar cewa suna kokarin dakatar da Buhari

Majalisar ta karyata wannan rahoto tace sam ba ta ko fadi haka ba sharri ne kurum na mutane. Sanata Sabi yace wasu ne kawai ke yada irin wadannan karyayaki a kasa na cewa Majalisa za ta je kotu ta nemi a tsaida wannan Gwamnati.

A wannan makon ne dai shugaban Hukumar kwastam na kasa Hamid Ali mai ritaya yace ba zai je Majalisa ba. Bayan nan shi ma Sakataren Gwamnati Babachir Lawal yace ba zai hallara gaban Sanatocin ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel