Wani babban Sarki a Arewa ya rasu

Wani babban Sarki a Arewa ya rasu

– Wani babban Sarki a Arewacin Najeriya ya kwanta dama

– A jiya ne dai aka rasa Sarkin Deba

– Mai martaba Abubakar Waziri ya rasu yana shekara kusan 80

Wani babban Sarki a Arewa ya rasu

Wani babban Sarki a Arewa ya rasu

An yi wani babban rashi a Arewa da ma kasar Najeriya gaba daya inda aka rasa wani babban Sarki daga cikin mayan Sarakunan Yankin a jiya Alhamis 23 ga watan Maris 2017. Wannan Sarki dai ya dade kan karagar mulki.

Sarki Abubakar Waziri na kasar Deba da ke Jihar Gombe ya rasu ne a wani asibiti da ke Garin Abuja. Mai martaba ya shafe shekaru 33 yana mulki a kasar. Allah dai yayi masa cikawa ne yana mai shekaru kusan 80 a Duniya.

KU KARANTA: An yi Jana'izar mutane 22 da mota ta buge

Shugaban karamar hukumar Yamaltu/Deba ya bayyana rasuwar Mai martaba wanda ya mutu ya bar ‘ya ‘ya 27 da mata 2 da kuma jikoki da sauran ‘yan uwa. Sarkin na 36 ya karbi mulki ne a shekarar 1984 inda ya gaji kakan sa. Marigayi mai martaba dai tsohon Soja ne.

A dalilin irin kokari da gwagwarmaya da tsohon shugaba Cif Olusegun Obasanjo yayi a baya an yanke shawarar nada masa wata Sarauta.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel