Ruwa ya fara karewa dan kada: Masu saida Dala sun fara kuka

Ruwa ya fara karewa dan kada: Masu saida Dala sun fara kuka

‘Yan kasuwa masu canjin kudi sun fara kokawa da lamarin yayin da darajar Dala ya fara yin kasa. Idan ba ayi sa’a ba ma dai abubuwan na iya kara tabarbare masu nan gaba

Ruwa ya fara karewa dan kada: Masu saida Dala sun fara kuka

Ruwa ya fara karewa dan kada: Masu saida Dala sun fara kuka

Masu canjin dala sun fara wayyo-wayyo don kuwa darajar Dalar Amurka kasa kurum ke yi a wannan hali. Dalar ta sha kasan da ba ta taba yi ba tun kusan fiye da watanni 7 da suka wuce daga jiya zuwa yau dinnan.

Jaridar This Day ta bayyana cewa ana sayar da Dalar Amurka guda a kan kusan N400 a kasuwar canji tun jiya a wasu wurare. Yanzu ma dai rahotanni sun fara nuna cewa Dalar ta yi kasa da N400 a yau Alhamis.

KU KARANTA: EFCC: Gwamnoni 5 da ake zargi sun tafka sata

Gwamnan CBN Emefiele

Ruwa ya fara karewa dan kada: Masu saida Dala sun fara kuka

Wani wanda ya je sayen dalar ya bayyana cewa ‘yan kasuwar sun fara kuka don kuwa ta dumfari N385. Dalar dai ba ta taba lalacewa haka ba tun bara. Dama masu canji watau Bureau De Change sun ce abubuwa za su gyaru nan gaba.

Gwamnan CBN Godwin Emefiele yace CBN din na kokarin ganin darajar Naira bai kara fadi ba, yace kuma wannan ba abu bane da zai gagara. Jama’a da dama dai suna sukar tsarin harkar kudi na Gwamnna babban bankin amma yanzu da alamu za a samu sauki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel