Ashe Dino Melaye yayi halin bera lokacin da yake jami’ar ABU

Ashe Dino Melaye yayi halin bera lokacin da yake jami’ar ABU

- Rikicin da ke tsakanin Sanata Dino Melaye da jaridar Sahara Reporters ta kara tsami

- An bayyana cewa ya kaisu kotu saboda batancin da suke masa

Dino Melaye yayi satan talabijin lokacin da yake jami’ar ABU – Sahara Reporters

Dino Melaye yayi satan talabijin lokacin da yake jami’ar ABU – Sahara Reporters

Jaridar Sahara Reporters tayi ikirarin cewa an taba tsige Sanata Dino Melaye a matsayin shugaban daliban sashen Geography a jami’ar Ahmadu Bello saboda yayi satan sabon talabijin na dalibai.

KU KARANTA: Jami'ar ABU tayi amai ta lashe

A wata magana da jaridar tayu ta shafinta na Tuwita, tace daya daga cikin abokan Dino Melaye ne ta basu wannan labari.

Dino Melaye dai ya kasance cikin rikicin tun lokacin da jaridar Sahara Reporters ta wallafa wani labari cewa Sanatan bai karashe karatunsa a jami’ar Ahmadu Bello ba.

Tuni sanata Ali Ndume ya bukaci majalisar dattawa ta gudanar da bincike cikin al’amarin kuma ta fara.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel