An kammala shirin gina ma talakawa gidaje 180,000 kyauta a Najeriya - Daraktan ANDP

An kammala shirin gina ma talakawa gidaje 180,000 kyauta a Najeriya - Daraktan ANDP

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Kungiyar samar da cigaba a nahiyar Afirka, ANDP zata gina gidaje guda 180,000 a fadin kasar nan da zata raba ma talakawa kyauta ba ko sisi.

Gidajen za’a gina su ne masu dakuna biyu biyu, kuma za’a watsa sune a shiyoyi daban daban na dukkanin jihohin, sa’annan za’a gina musu makarantu, ofishin yansanda, kasuwanni da asibitoci.

Wannan kungiya ta ANDP wani sashi ne na tsarin cigaban duniya ta bayyana cewa zata raba gidajen ne ga talakawa kyauta, daraktan kungiyar mai suna Samson Omojuyigbe ya shaida ma kamfanin dillancin labaru, NAN cewa gidajen zasu lakume zambar kudi naira triliyan 2.8, sa’annan yace za’a gina gidajen ne guda 5000 a kowane jiha a kan naira biliyan 78.

KU KARANTA: ‘Muƙarraban Buhari, su ke munafuntarsa’ – Sanata Hamma Misau

Samson yace: “ANDP wata kungiya ce mai zaman kanta, kuma zata kashe makudan kudade wajen samar ma jama’an Afirka gidaje kyauta, musamman wadanda suke cikin halin matsin tattalin arziki. Mun gwammace mu gina ma talakawa gidaje kyauta, akan mu dinga kai kayyayin tallafi sansanin yan gudun hijira ana cinyewa.

“Zamu gina gidaje ciki biyu biyu har guda 5000 a kowane jiha na kasar Najeriya, abinda ya bamu kwarin gwiwar shigowa mu tallaha shine yadda gwamnatoci a kowane mataki suke fama da karancin kudi da ba zasu iya magance matsalolin jama’a gaba daya ba.

“Wannan ne yasa muka hada kai da kungiyoyi masu zaman kansu, tare da masu hannu da shuni don ceton al’umma ta hanyar sama musu rayuwa mai inganci. Ko sisin kobo gwamnati ba zata kashe a wannan harkar ba, face goyon baya da muke bukatar su bamu don samun nasarar aikin. Burin kungiyar mu kawai shine kawar da talauci daga nahiyar Afirka.”

Dayake bayani kan yadda za’a raba gidajen, Samson yace: “Ba zamu samu matsala wajen rabon gidajen ba, za muyi amfani da ilimin kimiyya wajen fitar da wadanda suka cancanci a basu gidajen ba tare da da nuna fifiko ga wani ko wasu ba, ba zamu yarda da sa bakin kowa ba a harkar rabon gidajen, saboda muna sa ran mutane su nuna tsoron Allah."

Mista Samson yace a yanzu haka jihohin Enugu, Ebonyi, Akwa Ibom da Kross Ribas sun bayar da filayen da za’ayi gine ginen, inda yace tuni an kaddamar da fara aikin gine ginen a kauyen Ikpa Nkanya na garin Kros Ribas akan wani katafaren fili eka 250 wanda gwamnatin jihar ta bayar.

Samson ya cigaba da fadin jihohin Kaduna, Kano, Jigawa da Adamawa sun yi alkawarin bayar da nasu filayen nan bada dadewa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel