Majalisa ta bukaci gwamnati ta sake gina titin Bauchi zuwa Yola

Majalisa ta bukaci gwamnati ta sake gina titin Bauchi zuwa Yola

- Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta sake gina hanyan Bauchi, Gombe zuwa Yola

- Majalisar ta umurni kwamitocin a kan aiki da kasafin kudi cewa suyi gagawar saka sake gina hanyan mai tagwaye a kasafin kudi na 2017

Majalisa ta bukaci gwamnati ta sake gina titin Bauchi zuwa Yola

Majalisa ta bukaci gwamnati ta sake gina titin Bauchi zuwa Yola

Majalisa wakilan Najeriya a ranar Laraba, 22 ga watan Maris ta bukaci ma'aikatar aiki da gidaje ga sake gina hanyar Bauchi, Gombe zuwa Yola don hana asarar rayuka da dukiya.

Majalisar ta kuma yi kira ga hukumar kula da hanyoyin gwamnatin tarayya (FERMA) cewa ta kula da hanyan har zuwa lokacin da gwamnati za ta fara sake gina hanyan.

Wannan ya biyo bayan motsi da dan majalisa Ali Isa daga jihar Gombe a karkashin jam’iyyar PDP cewa a kwai bukatar sake gina hanyan Bauchi, Gombe zuwa Yola.

KU KARANTA KUMA: Jami'ar ABU ta fasa magana akan takardar shaidan Dino Melaye

Isa ya bayyana cewa hanya ne kawai babban hanya da ta hada jihohin uku a Arewa maso gabas.

Ya kara bayyana damuwarsa, inda ya ce ‘yan fashi da ‘yan ta’adda na amfani da yanayin hanya don kai farmaki ga matafiya a yankin.

Sabili da haka, majalisar ta umurni kwamitocin a kan aiki da kasafin kudi suyi gagawar saka sake gina hanyan mai tagwaye a kasafin kudi na 2017.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel