Hotunan wata makarantar Firamari a Kaduna dake da ɗalibai 300, kujeru 15 kacal!

Hotunan wata makarantar Firamari a Kaduna dake da ɗalibai 300, kujeru 15 kacal!

Duk da kirarin da ake yi ma gwamnan jihar Kaduna na cewa yana daya daga cikin gwamnoni masu aiki a Najeriya, sai dai wasu cikin makarantun Firamrin jihar na cikin tsaka mai wuya.

Hotunan wata makarantar Firamari a Kaduna dake da dalibai 300, kujeru 15 kacal

Dalibai wata makarantar Firamari

NAIJ.com ta gano wata makarantar Firamari dake kauyen Gujeni, cikin karamar hukumar Kagarko, wanda ke da malamai kwara 6, amma daya daga cikinsu ne kadai ya je makarantar a lokacin da NAIJ.com ta isa makarantar.

KU KARANTA: ‘Muƙarraban Buhari, su ke munafuntarsa’ – Sanata Hamma Misau

Hotunan wata makarantar Firamari a Kaduna dake da dalibai 300, kujeru 15 kacal

Yan makaranta suna zauna a kasa

Ita wannan makaranta tana da rukunin azuzuwa guda 2, a rukuni daya akwai azuzuwa guda 2, inda a dayan rukunin akwai azuzuwa guda 2 hade da ofishin shugaban makarantar.

Hotunan wata makarantar Firamari a Kaduna dake da dalibai 300, kujeru 15 kacal

Dalibai basu da kujeru acikin aji

Gaba daya teburan makarantar masu hade da kujeru guda 15 ne kacal, yayin da jimillan daliban dake makarantar sun haura 200, don haka dayawa daga cikinsu a kasa suke zama don daukan darasi.

Hotunan wata makarantar Firamari a Kaduna dake da dalibai 300, kujeru 15 kacal

Ba wani kujera a aji

Wannan makarantar Firamari na Gujeni yana nan akan titin Kaduna zuwa Abuja, gab da babban titin data hada Kaduna da Abuja. don haka ake kira ga gwamnati data kawo agaji ga wannan makaranta, don taimaka ma rayuwar daliban.

Ga bidiyon nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel