An cafke babban kwamandan Boko Haram a Ado-Ekiti

An cafke babban kwamandan Boko Haram a Ado-Ekiti

- An kama wasu shugabanin ‘yan Boko Haram a jihohin Ekiti da Bauchi

- Jami’an tsaro ta ce an same wani daga cikin ‘yan ta’addar da bindiga kirar AK-47

An cafke babban kwamandan Boko Haram a Ado-Ekiti

An cafke babban kwamandan Boko Haram a Ado-Ekiti

Hadin gwiwar jami’an tsaro na soji da na hukumar tsaro ta farin kaya DSS, sun kama wani mutum da ake zargin babban dan kungiyar Boko Haram ne mai suna Adenoyi Abdulsalam a Ado-Ikiti babban birnin jihar Ikiti.

A sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Laraba, 22 ga watan Maris ta bakin Mista Tony Opuiyo ta ce an sameshi da bindiga kirar AK-47,yayin da ake kara yin bincike akansa.

Wanda ake zargin yana matakin karshe na shirya satar wasu manyan mutane a garin, domin karfar kudin fansa ,ya addabi al’ummomin jihar.

Ya kuma ce an kama wani dan kungiyar ta Boko Haram, Usman Rawa wanda aka fi sani da Mista X, a garin lafiya dake jihar Nassarawa ranar 17 ga watan Maris.

Ya ce Usman ya karbarwa Abdullahi Isa hayar gida a lafiya wanda sananne ne a akaita ta’adanci.

Ya ce, shirinsu shine na samar da wani sansani da daza su rika ta’addanci, satar mutane,da kuma fashi da makami a Abuja, Minna, da kuma makotan jihohi.

Ya cigaba da cewa hukumar ta kama babban kwamandan Boko Haram Nasiru Sani wanda aka fi sani da Osama a Bauchi ranar 15 ga watan Maris.

Sani ya tsere ne daga babban gidan yari na Bauchi a watan Oktoban 2010 inda ya boye a Maiduguri.

Opuiyo ya ce a kokarin hukumar na cigaba da kakkabe yan tada kayar baya, ta kama wani Adamu Jibrin a kasuwar Jeka-da-Fari Gombe ranar 13 ga watan maris.

Mutumin wanda yake amfani da sunan karya na Dantata, ya kasance dan aike tsakanin kwamandodin Boko Haram da yan Kungiyar. Mutumin ya tabbatar da kasancewarsa dan kungiyar ta Boko Haram.

Har ila yau, hukumar ta kama wani da ake zargi da samar da abinci ga Kungiyar Boko Haram, Ibrahim Fulata da abokan aikinsa 3 a Dutsen Tanshi dake Bauchi ranar 28 ga watan faburairu.

KU KARANTA KUMA: Kana bukatar ka sani abubuwa 5 game da harin ta'addancin UK da ya bar mutane 4 matattu

Opuiyo ya kara da cewa hukumar ta kama wadanda ake zargi yan kungiyar ta Boko Haram ne a Jihohin Kano,Kogi da Yobe.

Opuiyo ya tabbatarwa da yan Najeriya cewa zata cigaba da kare rayuka da dukiyoyinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel