Kasar Japan ta samar ma al’ummar jihar Kebbi ruwan sha bayan kwashe shekaru 300 basu da ruwa

Kasar Japan ta samar ma al’ummar jihar Kebbi ruwan sha bayan kwashe shekaru 300 basu da ruwa

Al’ummar kauyen Ubandawaki dake karamar hukumar Kalgo na jihar Kebbi suna cikin farin ciki ganin yadda suka samu famfon tuka tuka na farko bayan shekaru 300 suna fama.

Kasar Japan ta samar ma al’ummar jihar Kebbi ruwan sha bayan kwashe shekaru 300 basu da ruwa

Kasar Japan ta samar ma al’ummar jihar Kebbi ruwan sha bayan kwashe shekaru 300 basu da ruwa

Dagacin kauyen Malam Magaji Daggi ne ya bayyana haka yayin da ake bikin kaddamar da rijiyan burtsatsin, inda yace sun dade suna mafarkin ganin wannan rana, tare da yi ma wadanda suka gina rijiyan godiya.

KU KARANTA: Yansanda sun kama inyamurai 3 dumu dumu suna zuba ma waken da suke siyarwa fiyafiya

Kasar Japan ta samar ma al’ummar jihar Kebbi ruwan sha bayan kwashe shekaru 300 basu da ruwa

Gwamnan jihar Kebbi

Gidan Rediyon Freedom dake Kaduna ne suka dauko wannan rahoton, inda ta bayyana cewar Kamfanin samar da cigaba na kasar Japan ne suka dauki nauyin gina wannan burtsatsi, don taimaka ma al’ummar kauyen sakamakon basu da wata hanyar samun ruwa mai kyau idan ba wani rafin garin ba.

Shima shugaban hukumar samar da ruwan sha na jihar Kebbi Alhaji Muhammadu Gwandu ya tabbatar da lamarin, inda yayi ma kamfanin Japan da suka dauki gabaran taimaka ma jama’an kauyen ubandawaki da wannan famfon tuka tuka.

A ranar Laraba 22 ga watan Maris ne aka yi bikin ranar ruwa na duniya kamar yadda majalisar dinkin duniya ta tsara, inda ake wayar ma jama’a kai danganeda amfani da ruwa mai tsafta don kauce ma cututtukan da ka iya zuwa tare da wannan ruwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel