‘Muƙarraban Buhari, su ke munafuntarsa’ – Sanata Hamma Misau

‘Muƙarraban Buhari, su ke munafuntarsa’ – Sanata Hamma Misau

Sanata mai wakiltan mazabar Bauchi ta tsakiya Sanata Isa Hamma Misau ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shiga taitayinsa da mukarrabansa, saboda sun eke ci mai dundunyiya.

‘Muƙarraban Buhari, su ke munafuntarsa’ – Sanata Hamma Misau

Sanata Hamma Misau

Sanata Misau ya zargi na kusa da Buhari da kawar masa da hankali daga ciyar da kasar gaba ta hanyar cika alkawurran daya daukan ma al’ummar da suka zabe shi.

Sanata Misau ya bayyana haka ne yayin dayake mayar da martani ga wata wasika da ministan shari’a Abubakar Malami SAN ya aika ma majalisar dattawa, inda yake bayyana dalilansa na rashin bayyana gaban majalisar.

KU KARANTA: Buhari ya jajanta ma ƙasar Birtaniya sakamakon harin da aka kai birnin Landan a jiya

Sanata Misau yace, kafin dawowar shugaba Buhari gida Najeriya daga birnin Landan, kasar na zaune lafiya, baka jin labarin wasu hare hare, da haka ne sanatan ya danganta abubuwan dake faruwa ga wasu mukarraban shugaba Buhari, da yace basa kaunar cigabansa.

“Idan kuka lura da irin shawarwarin da wasu na kusa da gwamnati suke ba shugaban kasa, zaku fahimci suna kokarin karkatar mai da hankali ne daga yin aikinsa, a kwanaki 50 da shugaba Buhari ya kwashe a kasar waje, lokacin da mataimakinsa ke rike da gwamnati, kun ji labarin wani harin yan Neja Delta, ko na Fulani makiyaya?

“Yau sati 2 da dawowar shugaban kasa gida kenan, amma har mukarrabansa sun fara rikita kasar, ina so yan Najeriya su gane cewa makiyan wannan gwamnati sune na kusa da shugaban kasa. Wannan hargitsin da suke janyowa, suna yi ne don su kawar da hankalin shugaban kasa daga gudanar da aikace aikacen daya sanya a gaba.

“Ya zama wajibi jama’a su gane makiyan gwamnatin nan suna cikin fadar shugaban kasa, ina rokon yan Najeriya dasu fara yi ma shugaban kasa addu’a, saboda munafukansa suna nan tare da shi. Ku duba irin wannan wasikar da ta fito daga ofishin ministan shari’a, mutumin daya kamata ya kawo zaman lafiya tsakanin majalisa da bangaren zartarwa

“Amma sai ga shi yana hada kisisina da rikici tsakanin bangarorin biyu, idan dai har ministan shari’a zai iya aike ma majalisa irin wannan wasika, toh wani irin shawara yake baiwa shugaba Buhari kenan? Don haka makiyansa na tare da shi.” Inji Misau

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel