Ina duba zuwa ga ranar da yan Afrika zasu tattara litattafan Injila da Qur’anai sannan su kona su – Bisi Alimi

Ina duba zuwa ga ranar da yan Afrika zasu tattara litattafan Injila da Qur’anai sannan su kona su – Bisi Alimi

Shahararren dan luwadin nan na Najeriya mazaunin Landan, Bisi Alimi ya kuma fitowa don yin mummunan faruci game da yan Afrika da kuma addinin su.

Ina duba zuwa ga ranar da yan Afrika zasu tattara litattafan Injila da Qur’anai sannan su kona su – Bisi Alimi

Shararen dan luwadi, Bisi Alimi

Alimi, wadda ke auran wani bature, yaje shafin sa na Instagram yan sa’oi kadan a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris, don ya bayyana cewa yana duba zuwa ga ranar da yan Afrika a fadin duniya zasu fito da litattafansu na addini wato Injila da Qur’ani don su cinna masu wuta.

Ya rubuta: “Ina duba zuwa ga ranar da yan Afrika a fadin duniya zasu tattara litattafan su na Injila da Qur’ani sannan su kona su a kasuwa, yayinda muke neman sanin gaskiyar ko mu su wanene. Barka da safiya”.

KU KARANTA KUMA: Majalisar wakilan Najeriya ta gargadi shugaba Buhari kan wa’adin mulki

Kalli rubutun a kasa:

NAIJ.com ta tattaro cewa, Bisi Alimi ya buga a kan Instagram tare da taken: “Nauyi ne da ya tattara a kan yan Afrika matasa da tsofaffi da su tabbatar da cewa duniya ta dawo ga daukakar ta. Mu tuna cewa Turawa da sukayi amfani da Injila gurin bautar damu sun juya mata baya.”

KU KARANTA KUMA: Kudin Paris Club da aka maido: fadar shugaban kasa saki bayanai filla-filla, KALLI nawa ko wacce jiha ta samu

Kalli rubutun a kasa:

Kalli bidiyo na yadda shahararren dan wasan Nollywood ya bayyana cewa ya kusa zama fasto:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel