TURKASHI: Kungiyar na ‘yan babura ta yi alwashin dawo da hular kwano a Legas

TURKASHI: Kungiyar na ‘yan babura ta yi alwashin dawo da hular kwano a Legas

- Masu babura za su fara amfani da hular kwano a jihar Legas

- Shugaban kungiyar na ‘yan babura a jihar Legas ya ce saka hular kwano na iya kariyar matukin baburar

Kungiyar na ‘yan babura Nagari Nakowa da hadin gwiwar kungiyar na ‘yan babura masu zaman kansu (NNAMORAL) sun gama shirin domin dawo da hular kwano a jihar Legas ga mambobinta.

Shugaban kungiyar ta jihar Legas, Mista Suleiman Raji ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Legas cewa membobinta sun gane muhimmancin yin amfani da hular kwano.

Raji ya bayyana cewa saka hular kwano ko da yaushe na iya kariyar matukin babura da kuma rage tsananin raunin da ke faruwa daga hatsarorin baburar.

KU KARANTA KUMA: Yarinyar da aka haifa da kafa 4, da kuma laka 2 anyi mata tiyata

Ya ce: ‘’Gwamnatin jihar ce ta bullo da saka hular kwano a baya, kuma yanzu muna sake gabatar da shirin da kuma tilasta yin aiki da shi a tsakanin mambobin mu.’’

Raji ya yi kira ga gwamnati da ta samar wa kungiyar sababbin hular kwano na yanzu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel