Sojoji sun kashe Fulani 17 a Kudancin Kaduna

Sojoji sun kashe Fulani 17 a Kudancin Kaduna

Kungiyoyin Fulani da ke yankin kudancin Kaduna a Najeriya sun ce wasu sojoji sun kashe makiyaya 17 bayan da aka yi zargin cewa wasu Fulani sun kashe wani mutum.

Sai dai kakakin rundunar sojin Najeriya Laftanar Kanar Sani Usman Kuka-sheka, ya musanta wannan zargi, yana mai cewa babu yadda za a yi sojoji da ke kare rayukan jama'a, su rika kashe su.

Sojoji sun kashe Fulani 17 a Kudancin Kaduna

Sojoji sun kashe Fulani 17 a Kudancin Kaduna

Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah a yankin Malam Abdulhamid Musa Albarka ya shaida cewa sojojin sun yi wa rugagen Fulanin dirar-mikiya inda suka kama mutum takwas suka kai su bayan gari kana suka harbe su har lahira.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Anyi jana’izan yan kasuwa 22 da suka mutu a mummunan hatsarin mota

A cewarsa, baya ga wadannan mutanen, sojojin sun sake kama wasu mutanen, cikin su har da wata mace da kuma gurgu inda su ma suka kashe su.

Ya kara da cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Jama'a da ke jihar ta Kaduna.

Malam Musa Albarka ya ce mutane sama da 40 ne suka jikkata bayan wannan farmaki da sojoji suka kai.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta Kaduna, wacce ta ce ta samu labarin kisan, da ta dauki mataki a kan sojojin.

KU KARANTA KUMA: Majalisar wakilan Najeriya ta gargadi shugaba Buhari kan wa’adin mulki

Kudancin jihar ta Kaduna dai ya yi kaurin suna wajen rikice-rikice na addini da kabilanci da kuma siyasa, inda a wannan shekarar ya sake jan hankulan 'yan kasar sakamakon kashe-kashen da aka rika fama da su a yankin.

Kalli bidiyon rahotannin da tawagar NAIJ.com suka samo kan rikicin Kudancin Kaduna

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel