Wani dalibi ya rataye kansa bayan budurwar sa ta yaudare shi

Wani dalibi ya rataye kansa bayan budurwar sa ta yaudare shi

Wani dalibin makaranta ya kashe kansa ta hanyar rataya bayan budurwar sa ta kawo karshen soyayyar su.

Wani dalibi ya rataye kansa bayan budurwar sa ta yaudare shi

A cewar wani rahoto da ya iso ma hukumar NAIJ.com, wani dalibin makaranatar sakandare a Unganda ya rataye kansa bayan budurwar sa ta yaudare sa.

An bayyana cewa matashin da aka karya ma zuciya ya sami wani wasika daga budurwar sa wacce ta yanke shawarar kawo karshen soyayyar su. Wannan hukunci da ta yanke ya sa shi kashe kansa a take.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Anyi jana’izan yan kasuwa 22 da suka mutu a mummunan hatsarin mota

Ga abunda ya faru a cewar Jersey Sarprise wadda ya yada labarin a Facebook:

“Wani dalibin makarantar sakandare a Uganda ya kashe kansa bayan budurwar sa ta bar sa, a cewar wata wasika da idon shaida ya gano.

Wasikar ta kasance kamar haka: ‘Daga rana mai kamar ta yau dan Allah kada ka kuma zuwa gurina domin na samu wani saurayi da ya fi ka kyau.’

Saurayin ya kasa jure ma bakin cikin don haka ya yanke shawarar kashe kansa ta hanyar rataya.”

KU KARANTA KUMA: Majalisar wakilan Najeriya ta gargadi shugaba Buhari kan wa’adin mulki

Kwanan nan NAIJ.com ta hadu da mutumin da yafi karfi a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel