An kama mutane 7 da hannu cikin harin da aka kai birnin Landan

An kama mutane 7 da hannu cikin harin da aka kai birnin Landan

Jami’an yansandan kasar Birtaniya sun kama mutane 7 dake da hannu cikin harin aka kai a ranar Laraba 22 ga watan Maris wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 3 da jikkata wasu 40.

An kama mutane 7 da hannu cikin harin da aka kai birnin Landan

An kama mutane 7 da hannu cikin harin da aka kai birnin Landan

Sai dai shugaban yansandan kasar Mark Rowley yace an sake samun gawar mutum guda, hakan ya kai yawan wadanda suka mutu zuwa 4, yayin da 7 ka cikin halin wuya a asibiti.

Rowley yace yansanda na cigaba da bincike a wasu sassan birnin Landan, da Birmingham don gano wadanda suka aikata laifin.

KU KARANTA: Buhari ya jajanta ma ƙasar Birtaniya sakamakon harin da aka kai birnin Landan a jiya

“Muna da tabbacin wanda ta kai harin ita kadai ce, kuma harin ta’addancin da ake kaiwa a duniya ne ya tunzura shi daukan wannan mataki, zuwa yanzu bamu da wasu bayanai dake nuna akwai sauran barazana ga rayuwar jama’a nan gaba,” inji Rowley

Rowley ya shaida cewar akwai wasu mutane da ba yan kasar Ingila bane cikin wadanda aka hallaka, amma dai bai yi karin bayani ba.

Cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai dansanda guda da aka caka mai wuka, sai wasu manyan mata su biyu, sai kuma shi kanta wanda ta kawo harin.

Harin na ranar Laraba ya samo asali ne daidai lokacin da maharin ya buga motarsa da gadar Westminister, inda ya bubbuge mutane da dama, sa’annan ya ruga da gudu dauke da wuka ya caka ma dansanda.

Cikin wadanda suka jikkata akwai daliban sakandari yan asalin kasar Faransa, wadanda suka zo yawon yawon bude ido a kasar Ingila, inda suke tsammanin ministan harkokin kasashen waje na Faransa Jean-Marc zai kawo musu ziyara.

Zuwa yanzu dai an sanya dokar shiga yankin Westminister, kuma yansanda da dama sun bazama a yankin, kuma an sa ran za’a cigaba da zaman majalisa kamar yadda Firaministan kasar Theresa May ta bayyana, inda tace ba zasu bari yan ta’adda su tsara musu rayuwa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel