Sakataren gwamnatin tarayya ya kauracewa Majalisa

Sakataren gwamnatin tarayya ya kauracewa Majalisa

- Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya ki gayyatar da kwamitin majalisar dattawan kasar ta yi masa

- Lawal ya ce yaki gayyatar ne saboda ya tafi kotu domin ya kalubalanci gayyatar

- Kwamitin na zargin Lawal kan bayar da wasu kwangiloli ga wasu amininsa da kuma kamfanin da yake da hannun jari

Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya ce ba zai gurfana a gaban kwamitin dawainiya da al’umma a arewa-maso-gabas na majalisar dattawan kasar ba.

Lawal wanda aka shirya don ya bayyana gaban kwamitin a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris bisa zarginsa da cin hanci da rashawa.

Amma a ranar Laraba, 22 ga watan Maris sakataren ya rubuta zuwa ga Shehu Sani, shugaban kwamitin, da cewa ba zai amsa gayatar kwamitin ba saboda ya tafi kotu domin ya kalubalanci gayyatar.

A watan Disamba, 2016, sauren majalisar dattawan ta zargi Lawal da albazaranci da kudin da gwamnatin tarayya ta ware don taimakawa ‘yan gudun hijira a arewa-maso-gabas.

Kwamitin a cikin wata rahoto ta zargi Lawal da bayar da wata kwangila na miliyan 270 domin yanke ciyawa a jihar Yobe ga wani kamfanin da yake da hannun jari.

Kwamitin ta kuma yi zargin cewa, Lawal ya bayar da wasu kwangiloli ga wasu amininsa.

KU KARANTA KUMA: CBN za ta kawo karshen tashin dala

Majalisar dattijai sa'an nan ya kira domin ya yi murabus.

Amma shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi tir da al’amarin inda ya ce kwamitin ba ta yi wa Lawal adalci ba.

Sabilin maganan shugaba Buhari ya sa kwamitin majalisar dattawa ta gayyace Lawal ya bayyana a gabansa a ranar Alhamis domin kare kansa.

Amma Lawal ya ki gayyatar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel