Yansanda sun kama inyamurai 3 dumu dumu suna zuba ma waken da suke siyarwa fiyafiya

Yansanda sun kama inyamurai 3 dumu dumu suna zuba ma waken da suke siyarwa fiyafiya

Rundunar yansandan jihar Legas ta samu nasarar cafke wasu inyamurai su 3 masu siyar da wake mara kyau, wanda suke gauraya shi da fiyafiya.

Yansanda sun kama wasu inyamurai dumu dumu suna zuba ma waken da suke siyarwa fiyafiya

Yansanda sun kama wasu inyamurai dumu dumu suna zuba ma waken da suke siyarwa fiyafiya

An bayyana sunayen wadannan inyamurai wanda dukkaninsu yan uwan juna ne kamar haka: Faith, Chidioke da Sunday Ogbona, kuma an kama su ne bayan wata mata ta tsegunta ma jami’an yansanda, wanda ta kama su dumu dumu suna zuba ma waken nasu fiyafiya.

KU KARANTA: Soyayya: da gaske ne wannan gwamnan ya zama ‘mijin tace’?

Jaridar Punch ta ruwaito, sai da yansanda suka fara kama Chidioke da Ogbonna a ranar Juma’a 17 ga watan Maris, yayin da a ranar Lahadi aka kama yayansu wanda shine ubangidansu yayin dayake karbar belin kannensa.

Hukumar yansandan jihar Legas ta bayyana cewar, Faith yayi kokarin bayar da cin hancin N500,000 ga yansanda don a sakar masa kannensa, amma yansanda suka yi watsi da bukatarsa, nan fa suka yi ram da shi.

Yansanda sun kama inyamurai 3 dumu dumu suna zuba ma waken da suke siyarwa fiyafiya

Yansanda sun kama inyamurai 3 dumu dumu suna zuba ma waken da suke siyarwa fiyafiya

A ranar Laraba 22 ga watan Maris ne aka bayyana ma yan jaridu masu laifin a shelkwatar yansandan jihar Legas dake Ikeja, tare da wasu buhuhunan waken da kuma sauran fiya fiyan da aka gano a shagonsu.

Sai dai Chidioke mai shekaru 18 ya bayyana cewar suna yin hakan ne don kada kwari su shiga cikin waken:

“A tunanina fiyafiyan zai magance kwarin wake ne, don haka na zuba musu. Ina cikin zubawa kenan sai wata mata ta ganni, kuma ta gargade ni da in daina, bayan wasu yan mintoci ne sai yansanda suka diro shagon mu suka kama ni, kuma gaskiya yayana Faith baya nan sadda na zuba maganin.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel