Majalisar dattawa ta dakatar da binciken Babachir bayan yaki bayyana a gaban yan majalisa

Majalisar dattawa ta dakatar da binciken Babachir bayan yaki bayyana a gaban yan majalisa

Majalisar dattawan Najeriya ta ajiye shirin ta na bincikar babban sakataren gwamnatin tarayya David Babachir Lawal da kamfanin Rholavision kan kwangilar da ake zargi a kai.

Majalisar dattawa ta dakatar da binciken Babachir nayan yaki bayyana a gaban yan majalisa

Kwamitin Shehu Sani tace bata san ranar da zata ci gaba da bincike ba

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Lawal Bagaudu, sakataren kwamitin kula da walwalar yan gudun hijira a arewa maso gabas, da Shehu Sani ke jagoranta ne ya tabbatar da hakan, sanna kuma ya bayyana cewa an sanya sabon rana.

KU KARANTA KUMA: Majalisar wakilan Najeriya ta gargadi shugaba Buhari kan wa’adin mulki

Daya daga cikin dalilin da yasa aka daga shine cewa Rholavision ta bayyana a cikin wata wasika da ta aika ma kwamitin cewa ba’a samu ji daga manajan daraktan ta ba tunda yayi tafiya zuwa kauye kan mutuwar wani dan uwansa.

“An daka sauraron zuwa wani lokaci a nan gaba saboda ya zama dole shugaban kamfanin Rholavision ya hallara,” cewar Bagaudu.

NAIJ.com ta tuna cewa Babachir, wanda ya kamata ya gurfana a gaban kwamitin kula da walwalar yan gudun hijira a ranar Alhamis, 23 ga watan Maris domin ya yi bayanin zargin da akeyi a kan sa game da wasu kwangilan a sansanin yan gudun hijira a arewa maso gabas da basa bisa ka’ida, yace ba zai yi hakan ba.

Majalisar dattawa ta dakatar da binciken Babachir nayan yaki bayyana a gaban yan majalisa

Majalisar dattawa ta dakatar da binciken Babachir nayan yaki bayyana a gaban yan majalisa

Babachir Lawal ya rubuta wasika ga majalisar dattawa cewa ba zai gurfana a gaban ta ba duk da cewa aika masa sammaci.

KU KARANTA KUMA: An gano gidan alfarma na £2,000,000 a ƙasar Ingila mallakin tsohon babban hafsan sojan sama

Kwamitin kula da walwalar yan gudun hijira na majalisar dattawa ta bukaci sakataren gwamnatin tarayya Injiniya Babachir David Lawal daya gurfana gabanta don amsa tambayoyi dangane da wasu kudade da suka yi layar zana.

Kwanaki tawagar NAIJ.com ta shiga unguwanni sannan ta hadu da wani dan kasa dake ganin cewa shugaban kasar Najeriya ya fi kowa rashawa. Saurare shi.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel