Hukumar tsaro ta DSS ta kama wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram daya arce daga gidan yari

Hukumar tsaro ta DSS ta kama wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram daya arce daga gidan yari

Wani kasurgumin dan Boko Haram wanda ya taba tserewa daga gidan yarin jihar Bauchi a shekarar 201 ya sake shiga hannun jami’an tsaron sirri, wato DSS.

Hukumar tsaro ta DSS ta kama wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram daya arce daga gidan yari

Hukumar tsaro ta DSS ta kama wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram daya arce daga gidan yari

Cikin wata sanarwa da Kaakain hukumar DSS, Tony Opuiyo ya fitar yace jami’an su sun kama dan ta’addan mai suna Naisru Sani, wanda ake yi ma inkiya da suna Osama a jihar Bauchi a ranar Laraba 15 ga watan Maris.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a yau Laraba (Hotuna)

Kaakakin yace tun a shekarar 2010 ne kwamandan Boko Haram din ya tsere daga gidan yarin Bauchi, inda ya koma garin Maiduguri yana buya. Amma cikin kokarin hukumar DSS,bata yi kasa a gwiwa ba, har sai da ta kamo shi.

Hukumar tsaro ta DSS ta kama wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram daya arce daga gidan yari

Hukumar tsaro ta DSS ta kama wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram daya arce daga gidan yari

Mista Opuiyo yace hukumar ta smau nasarar kama wani kwamandan Boko Haram shima mai suna Adamu Jibrin a kasuwar Jeka-da-fari na jihar Gombe a ranar 13 ga watan Maris, ya cigaba da fadin shi dai Adamu Jibrin yana amfani da sunan bogi Dantata Sule, kuma shine mai kai sako tsakanin yan Boko Haram da kwamandojinsu. Kuma tuni ya tabbatar da cewa shi dan Boko Haram ne.

Bugu da kari, Kaakin DSS yace jami’an hukumarsu sun kara kama wani dan Boko Haram mai suna Ibrahim Fulata tare da wasu abokanansa guda 3 a unguwar Dutsen Tanshi dake jihar Bauchi a ranar 28 ga watan Feburairu.

Daga karshe yace ana nan ana gudanar da bincike wakan dukkanin wadanda aka kama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel