Gwamnatin tarayya ta wanke masu Coca-Cola

Gwamnatin tarayya ta wanke masu Coca-Cola

Gwamnatin tarayya kara magana game da lafiyar lemun nan na Coca Cola. Ministan lafiya na Najeriya ne ya wanke masu lemun kwalban

Gwamnatin tarayya ta wanke masu Coca-Cola

Gwamnatin tarayya ta wanke masu Coca-Cola

Ministan lafiya ya bayyana cewa a cigaba da shan lemun zakin nan na Coca Cola da kuma Sprite da Fanta don kuwa ba su da wati illa kamar yadda aka yi ta yadawa a kwanaki. Ministan yayi kashedi da kamfanin da su rika bayani idan har akwai abin da ka iya jawo matsala.

Hukumar kula da lafiyar magunguna da abinci watau NAFDAC da kuma Hukumar SON mai tabbatar da nagartar kaya a kasar tayi wani binciki inda ta gano cewa babu wata matsala wajen shan lemu irin su Coca Cola.

KU KARANTA: An yi Jana'izar mutane da dama da aka kashe

Gwamnatin tarayya ta wanke masu Coca-Cola

Ministan lafiya yace a sha Coca Cola babu laifi

Misis Boade Akinola ta Ma’aikatar lafiya ta bayyanawa manema labarai cewa bincike da aka yi ya nuna cewa sinadarin da ake gudu na Benzoic acid da ke cikin lemun bai da wani yawan da har zai yi illa a jikin mutum. Ana ta jita-jita a baya dai cewa irin su Coca Cola din da illa.

Sai kuma Hukumar gudanar da zabe na kasa watau INEC tace da na’ura za ayi amfani a wajen shirya zabe mai zuwa da za ayi a shekarar 2019. Hukumar tace wannan zai kawo karshe ko raguwar magudin zabe.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel