CBN za ta kawo karshen tashin dala

CBN za ta kawo karshen tashin dala

CBN na kokarin ganin darajar Naira ba ta kara shan kasa ba Inji Gwamnan babban bankin kasar na CBN watau Mista Godwin Emefiele. Yace kuma CBN din na da ikon yin hakan

CBN za ta kawo karshen tashin dala

CBN za ta kawo karshen tashin dala

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN yace suna da karfin hana darajar Naira ya kara sauka. Gwamanan yace dalilin da ya sa aka fara sakin daloli shine domin farashin kudin waje su tsaya daidai ba tare da wuce kima ba

Godwin Emefiele yace CBN din na kokarin ganin darajar Naira bai fadi ba, yace kuma wannan ba abu bane da zai gagara. Jama’a da dama dai suna sukar tsarin harkar kudi na Gwamnna babban bankin.

KU KARANTA: Majalisa ta gargadi shugaba Buhari

Mista Emefiele ya bayyana wannan ne ga manema labarai bayan an fito wani taro inda CBN ta yanke hukunci game da sha’anin darajar kudin kasar. Kusan mako hudu kenan CBN na ta cigaba da sakin miliyoyin daloli domin a biya bukatar jama’a wanda hakan ke sa dalar tana sauka kasa.

Gwamnan CBN yace asusun kudin wajen Najeriya yana ta kara bunkasa don haka za su cigaba da wannan kokari. Masu canji dai sun ce hakan ya taimaka wajen gyara lamarin don kuwa da yawa za su saki Dalolin da suka boye. A yanzu haka, bayanai da mu ke samu sun nuna cewa ana sayar da Dala guda a kusan N400.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel