Melaye zai kai jaridar Sahara Reporters kotu

Melaye zai kai jaridar Sahara Reporters kotu

Sanata Dino Melaye da safen nan zai kai karan jaridar Sahara Reporters , jaridar Vanguard ta bada rahoto.

Sanata Melaye zai kai jaridar Sahara Repoters kotu, zai bukaci diyyan batancin N5bn

Sanata Melaye zai kai jaridar Sahara Repoters kotu, zai bukaci diyyan batancin N5bn

Sanatan yace zai kaisu kotu akan laifin kokarin bata masa suna, tuhumar karyam da kuma wasu laifiuka daban.

Game da cewar masu magana da yawunsa, za’a kai karan babban kotun tarayya ne misalin karfe 9 na safe.

KU KARANTA: Sanatocin da suka bukaci Hameed Ali yayi murabus

Lokacin da jaridar Vanguard ta tuntubesa, Dino Melaye yace har yanzu bai kama shawaran cikar da aran ba da safen nan.

Zaku tuna cewa jaridar Sahara Reporters ta wallafa wani labari cewa sanata Dino Melaye bai karashe karatunsa a jami’ar Ahmadu Bello ba.

Wannan abu ya tayar da kura a majalisan dattawa ranan Talata inda sanata Ali Ndume y nemi majalisan ta gudanar da bincike cikin al’amarin.

Kana kuma an baiwa kwamiti umurnin gudanar da bincike cikin al’amarin.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel