Mayakan Boko Haram sun raba kan su a manyan motoci 7, da Babura 40 a kusa da Magumeri, Borno

Mayakan Boko Haram sun raba kan su a manyan motoci 7, da Babura 40 a kusa da Magumeri, Borno

Bayan bam din sassafe da aka saka a Maiduguri, jihar Borno a ranar Litinin, 22 ga watan Maris, jinsin masu fasaha a Maiduguri sun bayyana cewa kauyawa sun gano kimanin manyan motoci bakwai da Babura 40 jere dauke da yan ta’addan Boko Haram a jiya, 21 ga watan Maris.

Mayakan Boko Haram sun raba kan su a manyan motoci 7, da Babura 40 a kusa da Magumeri, Borno

Kauyawa sunyi ikirarin cewa sun ga yan ta'addan Boko Haram a kusa da Magumeri

Majiyoyin tsaro a Maiduguri, jihar Borno sun ruwaito cewa kimanin manyan motoci kiran Hilux guda bakwai da Babura 40 aka gano a jere dauke da yan mayakan Boko Haram a daren jiya inda suka doshi hanyar kauyukan Yakku da Afari, kimanin kilomita 30 daga karamar hukumar Magumeri, inda yan ta’addan suka kai hari a makon da ya gabata.

KU KARANTA KUMA: Mugun nufi: Yadda aka nemi a kashe shugaba Buhari

Mazauna yankin ne suka sanar da labarin ga majiyoyin tsaro a ranar Laraba.

Mazauna garin sun kuma bayyana cewa a koda yaushe tattaruwan yan ta’addan Boko Haram na nufin zasu kai wani mummunan hari ga kauyuka ko mutanen da yan ta’addan ke hara.

Sun ci gaba da bayyana cewa, akwai yiwuwar cewa mayakan na Boko Haram na shirin kai sabon hari a wani gari tsakanin yankin Gubio ko Gajiram ko kuma ko wani gari a tsakanin yankin na arewacin Borno kamar yadda tafiyar su ke nuni.

A yanzu an bayyana cewa an aika rundunar soji domin su kare yawanci kauyuka da garuruwan da ake zaton mayakan na iya kai hari.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel